Lauyoyin jami’iyar adawa ta NDP ta uwargidan tsohon shugaba Rawlings ce suna shirin shigar da kara a kotu a birnin Accra yau Alhamis, a kan hukuncin da hukumar zabe ta yanke na hana uwargidan tsohon shugaba Rawalings Nana Konadu Agyemang (AJIMAN) Rawlings bata cancanci ta tsaya takara a zaben shugaban kasa da Ghana zata yi ranar Bakwai ga wata Disamba.
Majalisar Dokokin Burundi ta amince da wani kudurin doka da gagarumin rinjaye, na ficewar kasar daga jerin kasashen da su ka amince da halarcin Kotun Manyan Laifuka ta Duniya (ICC), na baya-baya nan a matakan ware kanta daga al'ummar duniya.
A dai dai lokacin da gwamnatin tarayyar Najeriya ke bada tabbaci da kuma karfin gwiwa ga bangaren shari’a na Najeriya, cewa binciken da ake yiwa bangaren Shari’a ba anayi bane don rage karfin Shari’a ko tozarta Alkalai bane illa yaki da cin hanci da rashawa.
Kalaman da gwamnan jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello yayi akan lalacewar hanyar da ta hada Minna fadar gwamnatin jihar da kuma Abuja birnin tarayya ya hargitsa babbar jam’iyyar Adawa a jihar PDP.
Bayan da gwamnatin kasar Bangladesh ta fito filli da tayin baiwa duk wani dan yakin sa kai daya tuba tukucin kudi, hukumomi sunce wakilai guda biyu na wata mumunar kungiyar yan ta’ada, sun bada kai.
Masu nazarin al’amurra a kasar Syria, sun ce jiya Talata jiragen saman yakin Rasha samfurin jet, suka koma ga yiwa gundumomin da suke hannun yan tawaye a birnin Aleppo da yaki ya daidaita, luguden bama bamai, suka auna wasu unguwanin yan tawaye guda biyu harma suka kashe fiye da mutane ashirin.
An bada rahoton cewa wasu yan bindiga da suka yi shigar burtu sanye da rigunan yan sandan kasar Afghanistan sun kutsa wani wurin ibadar yan Shi’a dake cike da mutane a jiya Talata, da dare suka kashe mutane goma sha hudu da raunana fiye da mutane talatin.
A makon jiya ne dai gwamnatin jihar Borno ta bada sanarwar sake bude makarantun kwana na fadin jihar baki daya, wadanda aka rufe tun shekaru biyun da suka gabata sai dai yanzu haka ana samun jan kafa wajen komar dalibai musamman ma wadanda aka canzawa garuruwa zuwa garin Maiduguri.
Hadaddiyar kungiyar masu sarrafa kayan amfanin gona a Najeriya ta bukaci shugaban babban Bankin Najeriya ya yi murabus, dalilin gazawa wajen tabbatar da dorewar kamfanonin cikin gida a kasar.
Yayin da gwamnatin jihar Kaduna ta haramta kungiyar ‘yan Shi’a, masana harkar shari’a da kuma zaman takewa na kira ga gwamnatocin jihohin da ayi karatun ta natsu.
Gwamnatin Ethiopia tana zargin Masar da iza yan tawayen kasar, wanda hakan ya tilastawa Ethiopian ta kafa dokar ta baci a shekaranjiya Lahadi.
Faransa tace yana yuwuwa Rasha ta fuskancin tuhumar laifukan yaki saboda ruwan bama bamai da take yi a gabasin birnin Aleppo dake gabascin Syria.
Yanzu haka dai da alamun kama alkalai bakwai da jami'an tsaron farin kaya na SSS, suka yi na ci gaba da janyo cece-kuce a tsakanin lauyoyin Najeriya, inda wasu ke goyon baya wasu kuma na yin tur da kamen.
Sama da garuruwa 62 ne ambaliyar ruwan sama tayi awon gaba da su a jihar Neja dake tarayyar Najeriya, duk da yake dai babu asarar rayuwa amma ambaliyar ruwan ta jefa dinbim mutane cikin damuwar rashin muhalli.
‘Yan kungiyar Shi’a sun ci gaba da zanga zangar neman sako shugabansu Mallam Ibrahim El-Zakzaky a Abuja, kwanki biyu byan soke irin wannan zanga zanga da sauran ayyuka da suka shafi hakan na kungiyar a jihar Kaduna.
Domin Kari