Noma Tushen Arziki
Jiya ‘yan takaran shugaban kasa a zaben wannan shekara a Amurka, Hillary Clinton da Donald Trump sun yi muhawarsu ta biyu inda suka gwabza akan batutuwa da dama da suka shafi halin zaman rayuwar, shirin kiyon lafiya na shugaba Obama da kuma matsayin danatakar Amurka da kasashen ketare.
Wani jirgin soji mai saukar ungulu ya yi hadari a Arewacin kasar Afghanistan kuma ya hallaka mutane Bakwai dake cikinsa.
Gwamnatin Ethiopia ta kafa dokar ta baci ta tsawon watanni shida, a wani matakin maida martani ga tarukkan zanga zangar kin jinin gwamnati wda aka jima ana gudanarwa a sassan kasar daban-daban.
Dan takarar shugabancin kasa a Ghana a karkashin jami’iyar adawa ta APC ya yi alkawarin kafa gwamnatin hadin gwiwa, wanda a cewarsa itace kadai hanyar da za a bi wurin magance kalubaloli da kasar al’umman kasar ke fuskanta.
Fadar White House ta shugaban Amurka tace gwamnatin shugaba Obama zata fara nazarin goyon bayan da take baiwa yakin da rundunar hadin guiwa ta sojan kasa da kasa a karkashin jagorancin Saudi Arabia ke gudanarwa a kasar Yemen.
Wasu ‘yan Majalisar Najeriya na kiran nuna fahimta ga Majalisar Dattawan musamman kan kudurin dokar daidaito ga maza da mata a wajen ilimi, gado, aure, mukamai da dai sauransu, wanda ya kai karatu na biyu a majalisar.
Gobara ta lashe wani bangaren jami’ar Jos, lamarin da ya janyo asarar wasu muhimman takardu da sakamakon jarabawar ‘dalibai na kusan shekaru 40.
Yayin da tafkin Chadi ke ci gaba da samun koma baya, kasar China tayi tayin tallafawa kasashen yankin don sake farfado da tafkin.
Ranar 10 ga watan Oktobar kowacce shekara rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin tunawa da mutane masu tabin halkali a fadin Duniya.
An gudanar da taron masu ruwa da tsaki kan batutuwan da suka shafi cin zarafin mata da yara a jihar Kano.
Shugaba Barack Obama na Amurka dake kamalla mulkinsa a wannan shekara, ya sake yin afuwa akan karin fursunoni 102 da aka yanke wa hukuncin dauri a bisa laifukkan da ba’a taba lafiyar wasu ba.
A jiya ne aka tuhumci wasu mutane da suka hada sojojin Amurka shidda da wasu fararen hula da laifin satar kayan aiki da makamai na rundunar sojan Amurka da kuma sayar da su ga wasu mutanen kasashen ketare da suka hada da China, Rasha da Ukraine.
Kungiyar Tarayyar Turai ta bada sanarwar kafa wata sabuwar Hukumar Iyakoki da zata rinka sa dogarawa suna zagaya kan iyakokin kasashen Turai don hana shigowar ‘yan gudun hijira daga kasashen Afrika da na Larabawa.
Watakila kafin a kai lokacin shagulgullan Kirsimetin wannan shekara, an gama shafe birnin Aleppo na kasar Syria daga doron kasa – muddin Syria da Rasha basu ja burki ga fatattakar da suke yi wa birnin da jiragensu na yaki ba, a cewar manzon MDD na musammam na Syria, Staffan de Mistura.
Ana anfani da kalmomi iri, kamar “Dodo” ko “Babban Bala’in da ba’a ga kamarsa ba a cikin shekaru 100” wajen bayyana masifar dake tattare da wata mahaukaciyar guguwa mai iska mai karfin gaske da aka zana wa suna “Matthew” da yanzu haka take fattatakar wasu sassa na Amurka, musamman gabashin jihar Florida.
Gamayyar kungiyoyin ci gaban al’uma dake rajin sake gina yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, sun yi kira ga hukumomin yaki da almundahanar kudaden Jama’a na EFCC da ICPC su kaddamar da bincike kan zargin ofishin sakataren gwamnatin tarayya da badda sawun Naira Biliyan Daya da Miliyan Dari Uku kudaden tallafawa ‘yan gudun hijira da kuma aikin sake gina yankin Arewa maso Gabashin Najeriya da mayakan Boko Haram suka daidaita.
Kungiyar Krista ta Ghana ta hada gwiwa da ofishin Shugaban musulman kasar don ganin cewa an gudanar da zaben kasar na wannan shekara cikin aminci da luman.
Rahotannin da bana hukama bane na nuna cewa an zabi tsohon Fara Ministan Portugal Antonio Guterres, ya zama sabon babban sakataren MDD.
A jiya Laraba Rasha ta dakatar da yarjejeniyar shekaru uku da ta kulla da Amurka a kan makamashin nukiliya da nazarin harkokin makamashi, abinda ake ganin kamar wani mataki ne da zai kara lalata dangatakar diplomasiya a tsakanin kasashen biyu.
Domin Kari