Murnar da ‘yan matan Chibok 21 da iyayensu sukayi a Abuja a taron godiya da murnar samun ‘yanci bata misaltuwa, don ‘daya daga cikin iyayen matan ma ta sanya zani ne ta goya ‘yarta tamkar jaririya.
Wakilin sakataren harkokin wajen Amurka na musamman akan harkokin hulda da musulmin duniya, Mr Shaarik Zafar, zai gabatar da jawabi ga taron malaman addinin musulinci dana Kirista a birnin Kano game da rawar da malaman ke takawa wajen yaki da rashawa a tsakanin al’umma.
Noma Tushen Arziki
Shugaban Rasha Vladmir Putin ya musunta sabon zargi Amurka na cewa ita Rasha din tana kaiwa Amurkan hari a yanar gizo, kuma tana ba’a a kan barazanan daukar fansa da Amurka take yi idan Rasha tayi mata shisshigi a harkokin zaben Amurka dake tafe.
A wata sanarwa da ya dora a kan shafinsa na Twitter a jiya Lahadi ana sauran kimanin makwanni uku Amurkawa su yi zabe, dan takarar jami’iyar Republican Donald Trump, ya shaidawa magoya bayansa cewa an riga an yi masa magudi a zaben.
A jiya ne, a Najeriya, iyayen wasu daga cikin ‘yan matan Chibok da suka sami ‘yancin kansu, suka yi ta tsallen murna bayan da aka maido musu ‘ya’yan nasu da yan ta’adda suka sace, kuma suka yi garkuwa da su sama da shekaru biyu.
Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, yace izuwa yanzu Amurka da kawayenta suna da damar daukar mataki na zabinsu a Syria, sai dai ya kara da cewa Amurka da Turai basu da ra’ayin amfani da karfin soji, duk da cewar Rasha taki kakkautawa da hare harenta a Syria.
Bayan da cece-kucen siyasa ya dakile aikin Madatsar ruwa ta Kafin Zaki Dam dake Jihar Bauchi tsawon kwashe shekaru da dama, a yanzu Gwamnatin Najeriya tace tana nan tana nazari akan yadda za a ci gaba da aikin, a kokarinta na bunkasa ayyukan noman Rani a kasar.
Fira Ministan Iraqi Haider al-Aabadi, ya bada sanarwar cewa An soma kaddamar da gagarumin fara kai hare haren soji akan mayakan ISIS don fitar da su daga birnin Mosul wanda ya jima a hannunsu.
Gwamnatin jihar Kaduna ta gargadi al’ummar jihar da su guji yada jita jita don gujewa dukkannin wani tashin hankali da ka iya tayar da zaune tsaye.
An kaddamar da wani littafi mai taken Boko Halal da jami’in rudunar sojan Ruwan Najeriya Abdulkareem Dawood ya rubuta don barranta daga duk wata manufa ta ‘yan Boko Haram.
Michelle Obama, matar shugaban Amurka Barack Obama, tace kalaman batanci kan jikin mata dake fitowa daga bakin daya daga cikin ‘yan takaran shugaban kasa a zaben wannan shekara, magangannu ne “na cin zarafi, masu ban tsoro kuma wanda ke da ciyo” a wurin matan.
Wani bincike da aka gudanar anan Amurka ya nuna cewa kashi 86% na Musulmin dake kasar duk sun kudurta cewa zasu fito su jefa kujrik’unsu a zaben shugaban kasar da za’ayi ran 8 ga wata mai fita na Nuwamba, a daidai lokacinda ake ganin kamar kyamar da ake nunawa Musulmi da Musulunci na karuwa a Amurka din.
A Nigeria, ana ta ci gaba da murna da kuma bayyana ra’ayoyi game da kubutar 21 daga cikin ‘yanmatan nan na Chibok da kungiyar Boko Haram ta sace, wadanda suka sami ‘yancin kansu har ma suka sadu da mataimakin shugaban kasar, Yemi Osinbajo jiya a Abuja.
Mutane 38 aka hallaka, aka raunana wasu fiyeda 50 a cikin wata mummunar tarzomar da ta barke ranar Larabar shekaranjiya a Junhuriyar Afrika ta Tsakiya.
Kwamitin sake nazarin tuhunce-tuhumce da ake yiwa masu zaman jiran Shara’a karkashin jagorancin alkalin alkalan jihar Adamawa, mai Shara’a Ishaya Banu, ya yiwa mutane 118 daga cikin 396 afuwa da ke gidan Yarin Jimeta.
Shugabannin kasashen duniya na ta ci gaba da aika sakkonin ta’azziya bayan mutuwar sarkin da akace yafi kowane sarki dadewa yana sarauta a duniya, watau Sarki Bhumibol Adulyadej, sarkin kasar Thailand.
Gwamnatin jihar Kaduna tace ta gano cewa kiyayya dake faruwa tsakanin mabiya addinin Krista dana Musulunci a jihar ta kan dasu ne tun a makaranta.
Wata fashewar da ta auku a Maiduguri, babban birnin jihar Borno ta Arewa maso Gabashin Najeriya, ta hallaka mutane akalla 8 a cewar hukumomi jiya Laraba.
Domin Kari