Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari ya kaddamar da kwamitin sake raya yankin Arewa maso Gabashin Najeriya karkashin jagoranci Janal T.Y. Danjuma Mai Ritaya, bayan da barnar ‘yan kungiyar Boko Haram sukayi a yankin.
Rundunar sojan Najeriya shiyya ta 7 dake garin Maiduguri, tace ta kame wasu mutane 30 da ke da hannu cikin satar Shanun Fulani wadanda suka hada da jami’an soja 4 da na ‘yan sanda 2 yayin da sauran suka kasance na fararen hula.
Majalisar Wakilai ta kafa kwamitin wucin gadi domin ya binciki matakan da Hukumar Tsaro ta farin Kaya ta dauka inda ta kai wa manyan Alkalan kasa farmaki cikin dare, saboda ana zargin su da cin hanci da rashawa.
Kasar Gambia ta zargi kotun bin bahasin laifuka ta duniya da laifin cewa tana juya bayanta ga “laifukkan yake-yake” da ake aikatawa. Kasar ta gambia tana wannan kalamin ne yayinda ita ma take ficewa daga kotun, watau ta bi sahun kasashe irinsu Afrika ta Kudu da Burundi, wadanda su ma a farkon watan nan suka janye kansu daga kotun.
Wani masani mai zaman kansa dake wa MDD aiki ya bayyana jin takaicin ganin cewa MDD din taki daukan alhaki, a shari’ance, na masifar cutar Kolera da ta barke a kasar Haiti, inda ta kama mutane 800,000, har ta hallaka fiyeda 9,300 daga cikinsu.
Wani mummunan farmakin ta’addanci da aka kai kan iyakar kasashen Kenya da Somalia ya yi sanadin mutuwar akalla mutane 12, a cewar wasu jami’an kasar Kenya.
Rasha tace zata kara tsawon lokacin da zata ci gaba da daina kai hare-haren jiragen sama akan birnin Aleppo na tsakiyar kasar Syria, inda tace su ma sojojin kasar dake biyayya ga shugaba Bashar al-Assad sun dauki irin wannan matsayin na jan burki daga kai hare-hare akan yankunan ‘yan tawayen kasar.
Rahottani daga Iraq na cewa mayakan adawa na IS yanzu sun dawo suna dogaro akan yankunan dake hannunsu a kasar Syria su aiko musu abinci da sauran kayan aiki a inda suke cikin Iraq, inda kasashen duniya ke bada tallafi don a kwace muhimmin birnin nan na Mosul.
Fadar Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari, ta maida murtani ga korafe-korafen da aka ce wasu ‘yan jam’iyyar APC mai mulkin kasar suna yi dangane da yadda take raba mukaman gwamnati.
Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari yayi wata ganawa ta musamman da wasu gwamnonin jam’iyyar APC, inda sukayi nazari da jinjinawa shugaban dangane da irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu.
Kungiyar Avengers ta ‘yan Niger Delta ta kaddamar da wani sabon hari kan kamfanin Mai na Chevron mallakar kasar Amurka.
Yayin da hukumar da ke kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ke bayyana wannan shekara ta 2016 da cewa itace mafi muni ga 'yan gudun hijira da 'yan cirani, yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya raba su da gidajensu daga jihar Borno, da yanzu ke sansanin yan gudun hijira a jihar Adamawa, sun bukaci da a hanzarta a maida su jihar su ta Borno.
Wasu yan bindiga da suka boye fuskokinsu sun kai hari a cibiyar horar da yan sandan Pakistan a kudu maso gabashin birnin Quetta, a jiya Litinin kuma sun kashe kuratan ‘yansanda sama da 40 da wani jami’insu, sun kuma raunata mutane sun fi dari.
Rundunar sojojin Iraqi ta kwace sama da kilomita 800 daga mayakan IS, tun lokacin da aka fara yakin sake kwato birnin Mosul a makon da ya gabata, a cewar jami’an Amurka a jiya Litinin.
Wani babban jami’in diplomasiya na Rasha yace Rasha ba zata kara yarda da wani shirin tsagaita wuta da sunan barin kayan agaji su shiga birnin Aleppo na Syria da yaki ya daidaita ba.
Dan takarar shugabancin Amurka karkashin jami’iyar Republican Donald Trump, wanda ke dada fuskantar matsaloli a kokarin da yake na lashe zaben, yanzu ya juya yana zargin abokiyar karawarsa Hillary Clinton da cewa tana shirya tattara ra’ayoyin jama’a na karya don aga tamkar itace kan gaba.
Hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta NDLEA tace ta kame wasu mutane dake kokarin safarar kwayoyi da tabar wiwi ga wasu ‘yan kungiyar Boko Haram dake a wasu kauyuka a jihar Borno.
Biyo bayan mika sunayen sababbin jakadu da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayi ga yan majalisar dattawa, yanzu haka cece-kuce ya barke a jihar Taraba inda jam’iyar APC, ta shugaba Buhari da kuma wasu yan siyasan jihar ke nuna kin amincewa da sunan da aka mika daga jihar na Mustafa Jaji, dan jam’iyar PDP.
Domin Kari