Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya WHO, ta shirya wa kasashen yankin Tafkin Chadi wani taron neman kawo karshen cutar Kwalara a yankin.
Noma Tushen Arziki
Jami’ai a Faransa suna shirin rosawa da kuma tada dukkan mutanen dake cikin wani sansanin yan gudun hijira da ke kusa da birnin Calais mai tashoshin jiragen ruwa dake Arewacin kasar.
Dubban matan kasar Venezuela sun gudanar da gagarumar zanga zangar lumana a kan titunan Caracas, babban birnin kasar ranar Asabar din shekaranjiya don nuna rashin jin dadinsu da dakatar da kuri’ar raba gardama wadda aka so ayi anfani da sakamakonta wajen saukar da shugaba Nicolas Maduro daga kan karagar mulki.
Wani sabon fada ya sake barkewa a jiya Lahadi a birnin Aleppo da sojoji suka kewaye, kwana uku bayan da aka dakatar da fadan don shiga da kayan agaji.
‘Yar takarar shugabancin kasar Amurka a karkashin jami’iyar Democrats Hillary Clinton wacce ke kyautata zaton lashe zaben da za’a yi a watan gobe, yanzu tayi watsi da abokin karawarta na Republican Donald Trump, kuma ta mayar da hankali wurin yakin zaben wakilan jami’iyarsu don samun rinjayi a manyan majalisun dokokin tarayya na Amurka din.
Mayakan Kurdawa da ake kira “Peshmerga” dake samun taimakon sojan atilere na kasar Turkiya, a jiya Lahadi sun kara samun nasara a kan mayakan IS dake wajen Mosul, birni mafi girma na biyu a kasar Iraqi, har ma a wani lokaci suka ce suna dab da garin Bashiqa.
An kammala babban taron wa’azi na kungiyar Izala ta kasa da kasa baki daya a jihar Kano.
Bayan da babban Alkalin Alkalan Najeriya mai Shari’a Mahmud Muhammad, yayi watsi da kiran da kungiyar lauyoyi tayi cewa ya kamata alkalan da ake zargi da aikata laifi su ajiye aiki har sai an gama bincike.
Yayin da dakarun sojin Najeriya ke ci gaba da fatattakar mayakan kungiyar Boko Haram a yankunan dake dajin sambisa, yanzu haka mayakan na karkatawa zuwa wasu kauyukan da babu sojoji.
Shugaban kasar Sudan ta Kudu, Silva Kiir, yayi barazanar cewa shi da kansa zaiyi jagorancin mayakansa suje su abkawa kungiyoyin tsageru dake tsakiyar kasar idan basu daina kai hare-hare akan fararen hular kasar ba.
Jami’an Hukumar zabe ta kasar Ghana na shirin ganawa da jagabannin jama’a da dattawa tare da shugabannin kafofin watsa labarai na kasar a cikin makon gobe don kaddamarda yakin wayar da kan jama’a dangane da babban zaben shugaban kasa da na ‘yanmajalisar dokokin da za’ayi ran 7 ga watan Disambar wannan shekarar.
Shugaba Barack Obama na Amurka yace nacewar da dan takaran jam’iyyar Republican azaben bana a nan Amurka, Donald Trump ke yi na cewa za’ayi mishi magudi a lokacin zaben, ba “abin dariya” bane.
Masana harakokin diplomasiya na kasa da kasa na nan suna ta kokarin fahimtar wani sako da aka sato daga taskar sakkonin email na ‘yar takaran shugabar kasa a zaben bana a nan Amurka Hilary Clinton, wanda ke nuna kamar tana zargin gwamnatocin kasar Saudi Arabia da Qatar da laifin bada goyon baya na kayan aiki da mankurdan kudade ga mayakan ‘yantawaye na IS.
Kasashen duniya sun zabura, suna sakawa gwamantin Syria da kawayenta sabuwar matsin lambar su ja burki ga bama-bamman da suke sakarwa garin Aleppo, don ma’aikatan bada agaji su sami sukunin shiga cikin birnin don tallafawa mazaunan garin da tarzomar ta rutsa da su.
Wasu ‘yan asalin Abuja daga gundumar Tunga Maje sun gudanar da wata zanga zangar lumana, inda sukayi korafin cewa rundunar sojan Najeriya na son mamaye musu filaye.
Kungiyoyi masu zaman kansu na lamuran kiwon lafiya sun dage kan kamfen din yaki da cutar dajin mama ko sankarar mama.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Borno EFCC tace ta samu nasarar kwato Naira Miliyan Dari da Casa’in da Shida da Dubu Dari Shida da Casa’in daga hannun mutane sakamakon irin takardun koke da suka karba daga hannun jama’a.
Gwamnatin jihar Neja ta kaddamar da wani kwamitin wayar da kan kungiyoyin addinin Musulunci game da kaucewa gudanar da ayyukan tunzura jama’a tsakanin al’ummar jihar.
Domin Kari