Rundunar sojan Najeriya shiyya ta 7 dake garin Maiduguri ta bayar da sanarwar mutuwar wasu jami’anta guda 5, sakamakon wani harin kwantar bauna da wasu ‘yan bidiga suka kai musu.
Faduwar darajar Naira a kasuwannin duniya ta gurgunta harkar fataken shanu a kasuwar shanu ta kasa da kasa dake garin Mubi, wanda ke kan iyakar Najeriya da makwabtanta na jumhuriyar Kamaru da Nijar.
A wani rahoto da jaridar Daily Trust ta rawaito na nuna yadda zazzabin cizon sauro ya ta’azzara a fadin Najeriya, inda kasar ke rasa kashi ‘Daya cikin Uku na adadin masu mutuwa sakamakon cutar, da kuma kashi ‘Daya cikin Hudu na jarirai a kasashen masu cutar ta Maleriya.
Noma Tushen Arziki
Hukumomin shara’a na Amurka sun cafke wasu mutane 61 da akace suna cikin rukunin wasu mazambata dake yawan kiran mutane ta waya, suna tsorata su don su basu kudi, inda kuma akace izuwa yanzu sun firgita mutane kamar 15,000, kuma sun tatsi makurddan kudade sun fi Dala Milyan 300 daga wurinsu.
A karon farko a tarihin siyasar Amurka, jiya matan shugaban Amurka guda biyu da suka hada da matar wani tsohon shugaban kasa tazo ta hade da matar shugaban kasa mai ci yanzu, sun hada karfi suna kyamfe mai alaka da zaben wannan shekarar na shugaban kasa.
Karshenta dai kasar Burundi ta dankawa Babban sakataren MDD Ban Ki-moon wasikar bayyana kudurinta na ficewa daga cikin Kotun Laifukka ta Duniya ta I-C-C dake a birnin Hague – kuma ministan harakokin wajen Burunndi din, Alain Nyamitwe, yace “alkalamin ya bushe, ba ja da baya akan wannan kuduri.”
Shugaba Paul Biya na kasar Kamaru ya kafa wata Hukumar Binciken da zata bi diddigin abin da ya janyo hatsarin Jirgin Kasan da ya faru a makon jiya inda mutane akalla 80 suka rasa rayukkansu, wasu kamar 600 suka jikatta.
Babban Sakataren MDD Ban Ki-moon, ya nemi a gudanar da bincike mai zurfi kan wani harin jiragen sama da aka kai ran Larabar shekaranjiya kan wata makaranta dake Syria, inda har aka hallaka mutane kusan 30, galibinsu duk yara kanana.
Kungiyar Kristocin Najeriya reshen jihar Neja tace ta gamsu da irin ci gaban da ake samu a wannan gwamnati, ta fuskar tsaro da yankin Arewacin Najeriya.
Majalisar Dokokin Najeriya ta zartas da dokar hana cin zarafi ko musgunawa ko tsangwamar 'ya'ya mata tun daga makarantun Firamare zuwa Jami'a tare da sa hukunci mai tsanani.
Kungiyar makiyaya ta Miyatti Allah a Najeriya ta koka akan matakin da tace gwamnatin jihar Ekiti ta dauka na haramtawa makiyaya kiwo a fadin jihar.
Kungiyar rajin kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta la’anci gwamnatin kasar Gambia saboda ficewarta daga kotun manyan laifuka ta kasa da kasa ta ICC, abinda Amnesty ta kira babban kalubale ga miliyoyin mutanen da ake cin zarafinsu a fadin duniya.
Shugaban cibiyar bada agaji ta MDD ya fada a jiya Laraba cewa yankin gabashin Aleppo na Syria, ya zama wani dandalin kisan al’umma, inda aka kashe mutane sama da dari hudu kuma kusan dubu biyu suka jikata a cikin watan da ya gabata.
Yar takara shugancin kasa a nan Amurka karkashin jami’iyar Democrats Hillary Clinton ta ninka abin da abokin karawarta na Republican Donald Trump yake kashewa na zunzurutun kudade a gwagwarmayarsu ta shiga fadar White House.
Fadar Shugaban Amurka ta White House ta ce har yanzu bata tuntubi gwamnatin Philippines akan barazanar da Philippines din tayi ba, na cewa tana neman yanke huldan harakokin soja dake tsakanin kasashen biyu.
A karon farko a tarihi, Amurka ta janye daga jefa kuri’a akan kudurin da aka gabatar a MDD na cire takunkumin tattalin arziki da kasuwanci da aka dorawa kasar Cuba tun kamar shekaru 60 da suka wuce.
Gwamnatin jihar Kaduna ta kaddamar da taron bitar wayarwa da matasa kai game da noman Alkama na rani, domin samar da ayyukan yi a jihar.
Matsalar rashin kudi da kuma tsadar rayuwa ta soma tilastawa wasu magidanta guduwa suna barin iyalansu, batun da yanzu ke kara barazana ga rayuwar ma’aurata.
Domin Kari