Fashi da makami, matsala ce da ke yawan addabar kasashe masu tasowa musamman ma a nahiyar Afirka. A 'yan kwanakin nan, mazauna yankin Agadez a Jamhuriyar Nijar, sun yi korafin cewa masu fashi da makami sun addabi dajin Agadez, lamarin da ke ci masu tuwo a kwarya.