Jama'ar yankin Santa Fe da wani dan bindiga ya kai hari, na ci gaba da jimami da addu'o'i ga mutane 10 da suka mutu daga harin na makarantar sakandaren da ke jihar Texas a Amurka.
Shirye-shirye sun kai kololuwa a auren Yarima Harry da amaryarsa Meghan Markle, wanda za a yi a garin Windsor da ke wajen birnin London a yau Asabar.
Sama da mutum 100 sun mutum bayan hadarin jirgin sama a kasar Cuba, yayin da wasu mutum uku suka tsira amma kuma suke cikin mawuyacin hali.
An fara tuhumar matashin da ya harbe dalibai tara a wata makarantar sakandare a Jihar Texas da wata malama guda daya.
Umurnin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayar na a fara tantance matafiya daga Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo da cutar Ebola ta bulla ka iya fuskantar tsaiko yayin da ma'aikatan kiwon lafiya a Najeriya ke ci gaba da yajin aiki, kamar yadda jaridun kasar suka ruwaito.
Masana a sassan duniya, na fadin albarkacin bakinsu, dangane da abin da ka iya biyo bayan hare-haren martani da Amurka, Birtaniya da Faransa suka kai a Syria.
An yi jana'izar Winnie Mandela, tsohuwar matar Nelson Mandela, wacce ta rasu a farkon watannan tana mai shekaru 81.
Yayin da ake ci gaba da tsokaci kan hare-haren da Amurka ta jagoranta a Syria, Amurkan ta kare kanta dangane da dalilan da suka sa ta kai harin.
'Yan Najeriya na ta bayyana ra'ayinsu dangane da sanarwar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi na sake tsayawa takara a zaben 2019, lamarin da yake shan yabo da suka.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya fadi dalilan da suka kawadaitar da shi har ya yanke shawarar cewa zai sake tsayawa takarar shugabancin Najeriya a 2019.
A wani mataki da ake ganin na samar da sauyi ne, gwamnatin Ethiopia ta rufe wani gidan yari da ya yi kaurin-suna, inda aka saki wasu fursunonin siyasa da kuma 'yan jarida.
Wata gobara da ta tashi a dogon benen gidan shugaba Donald Trumpda da ke New York ta halaka mutum guda ta kuma jikkata wasu ma'aikatan kashe gobara hudu.
Amurka ta dora alhakin harin makami mai guba da ake zargin dakarun Syria da kai wa a wasu yankunan fararen hula da ke Syria, lamarin da ya kai ga mutuwar mutane da dama.
Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta cika shekaru 70 da kafuwa, inda ta kwashe shekaru da dama tana yaki da cututtaka da ke addabar duniya, amma duk da wannan nasara, masana na ganin har yanzu akwai jan aiki a gaban hukumar.
Wani matukin wata motar kai sakonni, ya abka kan mutanen da ke tafiya a gefen titi a birnin Muenster inda har ya kashe mutane uku ya jikkata wasu, amma 'yan sanda sun ce ba a san dalilin harin ba.
Wata arangama da aka yi a karshen makon nan tsakanin dakarun Isra'ila da Falasdinawa a yankin Gaza, ta kai ga mutuwar mutane tara a cewar hukumomin lafiya na yankin Gaza.
Yayin da gwamnatin Mahamadu Isuhu na Jamhuriyar ta cika shekaru biyu a wa'adinsa na karshe, jami'an gwamnatin sun ce sun cika wasu daga cikin alkawuran da suka dauka a lokacin yakin neman zabe. Sai dai masu fafutuka na bayyana akasin hakan.
Bayan wani hari da maharan Boko Haram suka kai a yankin Balle Shuwa da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya, rundunar sojin kasar ta tabbatar da mutuwar mutane sama da goma.
Yayin da hukumomin Najeriya ke laluben hanyoyin da za su kawo karshen rikicin Boko Haram da ya ki ci ya ki cinyewa, Fadar shugaban kasar ta ce yin afuwa ga mayakan kungiyar zai iya zama alheri ga Najeriya.
Amurka ta dakile wani yunkurin gudanar da bincike kan zargin da ake yi na cewa Isra'ila ta yi amfani da harsashai na gaske wajen tarwatsa Falasdinawa masu zanga zanga a yankin Zirin Gaza a karshen makon da ya gabata.
Domin Kari