Takaddamar da ke tsakanin shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari da tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo, ta dauki sabon salo, bayan da Obasanjon ya yi zargin cewa gwamnatin na shirye-shiryen kama shi, zargin da gwamnatin ta Buhari ta musanta.
Anthony Bourdain kwararre a fannin girke-girke da ake watsa shirye-shiryensa a gidan talbijin na CNN, ya rasu. Bayanai sun ce Bourdain ya kashe kansa ne.
Kasa da makwanni biyu bayan da mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Alhaji Nuhu Gidado ya yi murabus daga mukaminsa, gwamnan jihar Muhammad ABubakar, ya zabi sabon mataimaki.
Amurka da China na yi wa junansu kallon hadarin kaji, bayan da Amurkan ta soki matakin mamaye yankin tekun kudancin Sin da China ta yi da dakaru da makamai.
Rahotanni daga Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo sun ce an sake samun wasu mutane biyar da suka kamu da cutar Ebola.
Kungiyar wasan kwallon kafa ta Ingila ta doke 'yan wasan Najeriya na Super Eagles da ci 2-1 a wasan sada zumunci da suka buga a Wembley yayin da ake shirye-shiryen gasar cin kofin duniya a Rasha.
Kwararru daga hukumar lafiya ta duniya WHO da takwarorinsu na kungiyar likitocin kasa da kasa, sun ce ana gab da shawo kan yaduwar cutar Ebola.
Najeriya da Ingila za su fafata yau Asabar a wasan sada zumunci a matakin ta da tsimin gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a wata nan na Yuni.
Amurka ta hau kujerar na-ki a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, kan wani kuduri da Kuwait ta gabatar da ya nemi a bai wa Falasdinawa fararen hula kariya.
Hatsaniya ta barke a wani taron jam'iyyar APC da aka yi a jihar Ekiti, lamarin da ya kai ga wani dan sanda ya yi harbin kan mai uwa da wabi, har ya samu wani tsohon dan majalisa.
Kasar Venezuela ta saki wasu Amurkawa biyu da ta tsare a matsayin fursunoni tun a shekarar 2016, bayan da ta tuhume su da laifin boye makamai a kasar.
Fadar White House ta ce mambobin gwamnatin Amurka suna kan shirye-shirye game da yadda ganawar Amurka da Korea ta Arewa za ta gudana, bayan da shugaba Trump ya ba da tabbacin cewa taron zai wakana.
A Najeriya, musamman ma a arewaci, hukumomi na daukan matakai daban-daban domin kaucewa rikicin makiyaya da manoma da yake kai ga asarar rayuka. A nata matakin, jihar Katsina ta yanke shawarar dasa fitilu a cikin dazuka.
Lura da yadda ake samun karin tabarbarewar harkar tsaro a jihar Zamfara, majalisar dokoki ta amince da a aikawa ma’aikatar tsaro da wasikar neman karin dauki saboda yadda ake ci gaba da samun hare-haren 'yan fashi.
A wani sakon Twitter da ya aike a daren jiya Juma'a, shugaban Amurka ya ce, akwai alamu da ke nuna cewa za a maido da shirin tattaunawar da zai yi da takwaran aikinsa na Korea ta Arewa Kim Jong Un bayan da ya soke ta a baya.
Kasashen kungiyar tarayyar turai sun samar da wata doka wacce za ta kare bayanan sirrin al'umar yankin tun bayan da aka samu kamfanin shafin sada zumunta na Facebook da yin sakaci da bayanan sirrin masu amfani da shafin.
Amurka ta koka da yadda ake samun matsaloli a yunkurin da take yi na yaki da ta'addanci a nahiyar Afirka, matsalolin da suka sa kasashen yammaci ba sa gane inda kungiyoyin 'yan ta'adda a nahiyar suka sa a gaba.
Murabus din da mataimakin gwamnan jihar Bauchi a Najeriya, Alhaji Nuhu Gidado ya yi, na ci gaba da jan hankulan jama'a, a daidai lokacin da gwamna Muhammad Abdullahi Abubakar ke musanta zargin cewa sabani suka samu a tsakaninsu.
Ga dukkan alamu, barakar da ta kunno kai a jam'iyya mai mulki ta APC a wasu jihohin Najeriya na kara fadada, tun bayan zaben mazabu da aka gudanar a kasar, yayin da masharhanta ke gargadin cewa hakan ka iya sa wankin hula ya kai jam'iyyar dare.
Cuba ta ayyana zaman makokin kwanaki biyu sanadiyar hadarin jirgin saman kasar da ya halaka mutane 107.
Domin Kari