“Kowa ya riga ya san cewa gwamna gogaggen ma’aikaci ne saboda haka ba zai yi irin wannan kuskuren na a zo a ce har za a ba shi cin hanci ko kuma na goro ba.” Inji Malam Garba, yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai bayan da gabatar da takardun bahasinsu ga kwamitin.
Shugaba Donald Trump yana so ya yi wa kundin tsarin mulkin Amurka gyara don kawar da dokokin da suka bai wa yaran baki da aka haifa a nan Amurka damar zama yan kasa.
Wannan shi ne karo na biyu da girgizar kasar ke aukuwa a birnin na Abuja. A farkon watan Satumba an samu makamancin hakan a unguwar Mpape.
An kai harin ne lokacin sallar Isha’i “bayan mun tashi daga sallar Isha’i ba mu samu damar komawa gida ba, da rarrafe ma muka fita daga garin.” Inji wani mazaunin garin a hirar da ya yi da Muryar Amurka.
Rundunar sojin ta Najeriya ta yi kira ga sauran mutum biyun da ake nema, da su yi hanzarin mika kansu domin ana bibiyan duk inda suke.
Sai dai hadakar kungiyoyin kwadagon kasar ta NLC ta yi watsi da wannan sabon tayi da Gwamnoni suka yi, inda suka ce suna kan bakarsu ta cewa sai an biya 30,000.00.
Akalla gwanayen ninkaya 40 aka tura karkashin ruwa domin neman ragowar jirgin na Lion Air, wanda ya bace daga na’urar da ke bibiyar jirage, mintina 13 da tashin shi.
Wannan ziyara ta Trump na zuwa ne a daidai lokacin da mambobin wurin ibadar da aka kai harin, wanda ake kira Tree of Life Synagogue suke gudanar da jana’izar farko ga mamatan.
Sanarwar ta kara da cewa, wannan karin dakaru, za su tallafawa jirage masu saukar ungulu biyu da aka tura domin tattara bayanan sirri.
Sanarwar ta kara da cewa mutum uku sun mutu daga bangaren ‘yan Shi’ar yayin da wasu dakaru biyu suka jikkata.
Robert Bowers ya bayyana ne a gaban kotun Magistrate akan keken guragu sa'o'i kadan bayan da aka sallamo shi daga asibiti sanadiyar harbin da 'yan sanda suka mai kafin su kama shi.
Akalla fasinjoji 189 da ma'aikatan jirgin sama lion air sun rasa rayukansu yayin da jirgin ya fada cikin teku mintina goma sha uku da tashin sa daka Jakarta babban birnin Indonesia.
"Muna neman hadin kan duk wanda ya san inda aka sake binne gawar.” Inji babban kwamandan rundunar sojin Najeriya ta 3 Division, Manjo Janar, B. A. Akinruluyo.
Kasar Turkiyya ta bukaci kasar Saudi Arabiya da ta bayyana ida suka kai gawar Jamal Khashoggi, sannan tana neman wani dan kasarta da aka yi amfani da shi wajan boye gawar.
Sabuwar dokar ta hana zirga zirga na zuwa ne bayan kisan da wasu masu garkuwa da mutane suka yi wa wani basarake a masarautar Adara, Dr. Mai Wada Galadima.
Kididdiga ta nuna cewa adadin 'yan Najeriya ya haura sama da miliyan 190 yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi hasashen cewa adadin zai haura miliyan 300 nan da shekarar 2050.
Gayyatar ta Ja’afar ta haifar da ra’ayoyi mabanbanta a tsakanin al'umar ciki da wajen Kano, musamman ma a shafukan sada zumunta kan tsaron lafiyarsa, inda yayin da wasu ke cewa kada ya je wasu kuwa suka nuna ya kamata ya akasin hakan.
Trump ya ce za a kaddamar da wani babban bincike karkashin gwamnatin tarayya domin zakulo wadanda ke da hannu a aikawa da wadannan sakonni na bam.
Sanarwar ta kara da cewa, hukumomin jihar sun dauki wannan matakin ne, bayan wani zama da aka yi a yau (Laraba) domin yin dubi kan yanayin tsaro a jihar.
Kafin ta musanta rahotannin, shafukan yanar gizon wasu jaridun kasar sun ruwaito Ministar tana cewa hukumomin Najeriya na kokarin samar da wani tsari da zai kayyade adadin yaran da mace za ta haifa a kasar.
Domin Kari