Kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC, ta yi barazanar sake shiga yajin aiki na gama-gari muddin ma'aikatan kasar ba su karbi Naira 30,000.00 nan da watan 11 na wannan shekarar a matsayin albashi mafi kankanci.
“Fadar shugaban Najeriya, karkashin jagorancin shugaba Muhammad Buhari na da karfin da za ta kare kan iyakokin kasar daga duk wata barazana.”
A makon da ya gabata, hukumomin Saudiya suka amince cewa lallai Khashoggi ya mutu a cikin ofishin jakadancin, inda a farko suka bayyana cewa ya gamu da ajalinsa ne bayan wata tarzoma da aka yi.
Yanzu haka ‘yan uwan marigayin, sun shigar da kara a caji ofis din ‘yan sanda inda suka nemi da bi masu Kadin danuwansu.
Sai dai jaridar Punch ta ruwaito cewa duk da kasancewar dokar, an kai hare-hare a unguwannin Narayi da Kaduna ta Kudu, inda aka zargi wasu mutane sanye da kayan soji da aikata kisa.
Rasha ta bayyana cewa ba ta karya ka'idodin yarjejeniyar kayyade harba makami mai linzami ba da suka yi da Amurka lokacin yakin cacar-baka, yarjejeniyar da Amurkan ke shirin ficewa daga ita.
Tuni dai rahotanni suka bayyana cewa hankula sun kwanta bayan da aka tura jami’an tsaro zuwa sassan jihar.
Magoya bayan kungiyar ta Juventus sun barke da sowa da nuna farin ciki a lokacin da Ronaldo mai shekaru 33 ya saka kwallon farko jim kadan bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.
“A matsayina na wacce ta yi ammana da abin da wannan gwamnati ta saka a gaba na nuna gaskiya, ya kamata na yi abin da ya dace na ajiye aikina.” Inji Kemi Adeosun.
Ma'aikatan sun yi boren ne na tsawon kwanaki uku, bayan da aka ki kebe masu lokacin zuwa su yi salla.
“Za a ci gaba da ganin tumbatsar ruwa a gabar tekun Carolina a yinin Asabar, a wasu yankuna ma har zuwa daren Lahadi da wayewar garin Litinin.” Inji Chris Wamsley, jami’i ne a hukumar da ke nazarin yanayi a Amurka.
Gabanin nada shi a matsayin jakadan Najeriya a kasar ta Qatar, Dr. Wase wanda masani ne kan harkar tsaro, ya sha ba da gudunmuwa a shirye-shiryen Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA) kan batutuwan da suka shafi tsaro.
Ana ci gaba da samun rahotanni masu karo da juna, kan bayanai da ke nuni da cewa, Ministar kudi a Najeriya, Kemi Adeosun ta yi murabus.
Tun kusan watanni uku kenan rikicin ya tsananta musamman a kananan hukumomin Barkin Ladi, Jos ta Kudu, Riyom da wasu sassan karamar hukumar Bassa
"Na maimaita wannan magana, don kusan cewa, wannan kokowa (fafutuka) inda aka dakatar da ita a ranar 1 ga watan Maris, daga nan za ta ci gaba." Inji Moussa Tchangari, daya daga cikin masu jagorar wannan tafiya.
“Ba su taba kowa ba, sun ce babu ruwansu da kowa,” sai dai sun yi ta neman jami’an tsaro, a cewar mutumin da ya yi magana da Muryar Amurka, wanda ya nemi a boye sunansa.
Rahotanni sun ce ta iya yiwuwa ruwan saman da aka yi ta tafkawa a 'yan kwanakin nan ne ya tilastawa giwayen suka yi kaura daga asalin yankunansu.
A ‘yan kwanakin nan, Adam Zango ya wallafa wasu sakonni makamantan wannan, inda a farkon makon nan ya rubuta wasu kalamai da ke nuni da cewa ya gane “munafukai” ne suke hada su fada.
“Wannan sun saka rayuwarsu ne cikin hadarin rasa ‘yancinsu na walwala akan warin takalmi daya da ba zai amfane su ba.”
“Har yanzu ina @officialPDPNigeria, ana ci gaba da tuntubar juna, mai girma #IbrahimShekarau, Sarudaunan Kano na musanta ficewa daga jam’iyyar PDP.” Shafinsa na Twitter ya bayyana.
Domin Kari