“Ina mai tabbatar muku cewa, ni ne (Buhari) na asali, a kwanan nan ma zan yi bikin cika shekaru 76 da haihuwa kuma zan ci gaba da kasancewa da karfina.”
Shugaba Buhari har ila yau, ya yi kira ga wadanda ba su samu nasara a zaben fidda gwani a jam'iyyunsu ba, da su fifita zaman lafiyar kasarsu sama da bukatunsu na kansu.
Rahotanni da dama sun ce sama da sojoji 100 aka kashe a wannan hari, ko da yake, rundunar sojin kasar ba ta fito ta fadi takamaiman adadin sojojin da ta rasa ba, duk da cewa ta tabbatar da aukuwar harin.
Kasashen na Amurka da Birtaniya da kuma kungiyar ta tarayyar turai sun ce za su sa ido su ga yadda wannan zangon gangamin yakin neman zabe zai kasance.
Lauyan gwamnan har ila yau ya nemi kotu ta dakatar da Ja’afar daga wallafa wasu karin hotunan bidiyo a nan gaba ta kowacce irin kafa.
Sanarwa ta kara da cewa duk da cewa an amince a saka hijabin, dole sai ya zamanto “gajere, tsabtatacce, kuma ya kasance launinsa ya yi daidai da launin kayan makarantar.”
Tsohon mataimakin shugaban Najeriyar, wanda zai yi takarar shugabancin kasar karkashin Jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, ya yi korafin cewa an ci zarafinsa saboda irin binciken da aka masa a filin tashin jirage na Abuja.
A yau litin ne wani dan kunar bakin wake ya kai hari inda ya kashe mutane 6 tare da raunata mutane 20 a wani yanki da mabiya mazhabar Shi'a su ke muzahara.
A jiya lahadi fada ya barke a tsakani 'yan tawayen Houth da kuma Sojojin kawance da Saudiyya kewa jagoranci, inda mutane bakwai suka rasa rayukan su har lahira.
Hukumomi a Najeriya sun ce sun fara shirin neman Birtaniya ta miko mata tsohuwar ministar mai Diezani Alison-Madueke, domin a tuhume ta kan zargin wawure kudin kasar da ake mata a lokacin tana ofis.
Tsarin da kasar ke bi shi ne, ‘yan kasar da Birtaniya ta mulka wadanda suka taba zama a kasar har na tsawon shekaru biyar ne kadai za su iya shiga rundunar sojin kasar.
Wani harin Ta'addanci da aka kai a garin Melbourne da ke Kasar Australia ya halaka mutun daya yayin da mutun uku suka jikkata.
Bayanai sun yi nuni da cewa maharan sun bude wuta akan motocin wasu matafiya sannan suka kona dogayen motoci da ke dauke da kayan abinci, kamar yadda shaidu suka bayyana.
“Tun da ya (karin albashi) shafi ma’aikata na gwamnati da na kamfanoni, su kamfanoni akan abubuwan da suke yi ne sukan kara farashin kayayyakinsu domin su samu kudaden da za su karawa ma’aikatansu.” Inji masanin tattalin arziki Yusha’u Aliyu.
Kwararru a fannin tattara ra’ayoyoin jama’a sun ce akwai alamu da ke nuna cewa jam’iyyar Democrat ta karbe rinjayen majalisar wakilai.
Wadanda suka yi garkuwa da daliban makarantar sun ce ba za su saki yaran ba, har sai sun cimma burinsu na samun ‘yancin gashin kansu.
A gobe Talata kungiyoyin ke shirin shiga yajin aikin na sai yadda hali ya yi, a wani mataki na nuna rashin jin dadinsu kan kin amincewa da gwamnati ta yi na biyan N30,000.00 a matsayin albashi mafi karanci.
Alkalin ya ce ya ba da wannan umurnin ne saboda a kaucewa mummunan tasirin da yajin aikin zai yi akan tattalin arzikin Najeriya, wanda aka shirya za a fara a ranar 6 ga watan Nuwamba.
Domin Kari