Mayakan Boko Haram sun sake lalata wasu turakun wutar lantarki a Maiduguri babban birnin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.
‘Yan wasan Super Eagles na Najeriya, sun samu damar shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka ta AFCON, wacce za a yi a Kamaru a bana.
Najeriya ce ke jagorantar rukunin L da maki takwas sannan Benin na biye da ita da maki bakwai.
“Najeriya za ta taimakawa duka makwabtanta wajen yaki da ayyukan ta’addanci.” Shugaba Buhari ya ce.
Wasu daga cikin jaruman Kannywood sun fara yin allurar riga-kafin COVID-19 yayin da ake ci gaba da aikin yin allurar a sassan Najeriya.
Dan wasan Tottenham Hotspur Gareth Bale ya ce zai koma kungiyarsa ta Real Madrid da zarar ya kammala wa’adin zaman aro da yake yi a London.
Akalla fararen hula 290 aka hallaka tun daga watan Janairu, adadin da ya haura yawan mutanen da aka kashe a shekarar 2020 a cewar Majalisar Dinkin Duniya.
Manchester City ta fara jin kamshin kofin gasar FA Cup, bayan da ta lallasa Everton da ci 0-2 a wasan da suka kara a zagayen Quarter Final.
Ga dukkan alamu, kurar da ta tashi bayan bikin karrama mawaka na Grammy da aka yi a Amurka a makon da ya gabata, ba ta kwanta ba, domin har yanzu ana ci gaba da ka-ce-na-ce musamman a Najeriya da aka karrama mawakanta biyu.
Samia Suluhu Hassan, ita ce mace ta farko da ta zama shugabar kasa a Tanzania mai yawan jama’a sama da miliyan 58.
A ranar Laraba mataimakiyar shugaban kasa Samia Suluhu ta sanar da mutuwar shugaba Magufuli, wanda ta ce ya yi fama da cutar bugun zuciya.
Hukumomin kwallon kafar kasar sun kwatanta Ibrahimovic a matsayin kwararren dan wasan da Sweden ba ta taba samun irin sa ba.
“Ko ta wacce fuska ka kalli wannan (lambar yabo,) babbar nasara ce ga Najeriya, al’adunta, da al’umarta! Ina taya dukkan wadanda suka samu wannan kyauta murna!" In Ji Davido.
A karon farkon tun bayan da ta karbi ragamar tafiyar da hukumar kasuwanci ta duniya WTO, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ta kai ziyara kasarta Najeriya.
Daliban kwalejin kula da harkokin gandun daji ta tarayya da aka sace a jihar Kaduna, sun yi kira ga gwamnati da ta cece su.
‘Yan Najeriya sun yi ta rige-rigen sayen man bayan da hukumar da ke kayyade farashi ta PPPRA, ta wallafa wasu alkaluma da ke nuna cewa za a kara kudin man zuwa naira 212.
Kungiyar Chelsea a gasar Premier League ta Ingila, ta zubar da damar da ta samu ta taka rawar gani a gasar, bayan da suka tashi canjaras da Leeds.
"Har iya tsawon wane lokaci za mu ci gaba da kasancewa a cikin wannan hali na matsalar tsaro? In ji Atiku.
Sabuwar wakar Namenj mai taken “Da ma” tana ci gaba da haskawa da jan hankulan masoyan wakokin zamani na Hausa musamman a shafukan sada zumunta.
Dan wasan kungiyar Paris Saint-Germain (PSG,) Angel Di Maria ya tsawaita kwantiraginsa da kungiyar har zuwa kakar wasa ta 2022.
Domin Kari