Jami’an tsaro da shugabannin al’uma a jahar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya, sun yi kira ga mazauna garin da su sa ido domin gano ‘yan Boko Haram da ake zargi suna kwararara zuwa kudancin kasar.
A yau Litinin, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya fara wata ziyarar kwanaki uku a kasar Faransa bayan da takwaran aikinsa Francois Hollande ya mika mai goron gayyata.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce kafin karshen wannan wata na Satumba, zai bayyana sunayen ‘yan majalisar zartaswarsa kamar yadda ya yi alkawari a baya.
Faransa na shirin shiga gamayyar dakarun da ke yaki da kungiyar Boko Haram, yayin da jiragenta suka fara sintiri a kasar Syria.
Rahotanni sun ce 'yan gudun hijrar na samun saukin ratsawa ta kasar Hungary fiye da yadda abin ya kasance a makon jiya, lokacin da aka ga alamar dai wannan kasa ta yankin tsakiyar Turai na shirin yin komai don hana 'yan gudun hijirar shiga kasashen Yammacin Turai mafiya arziki.
Gwamnatin Jahar Legas ta sake bullowu da dokokin tuka manyan ababan hawa na tankuna da masu daukan kaya masu nauyi domin kare aukuwar hadurra.
A Najeriya, akalla mahajjata 1,900 daga jahar Adamawa ake sa ran za su je kasa mai tsarki domin sauke farali, wadanda aka yi kira da su tuna da kasarsu a addu'oinsu.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sauka a kasar Ghana inda zai kwashe yinin yau yana tattaunawa da takwaran aikinsa John Dramani Mahama.
A Najeriya, har yanzu ana ci gaba da yin tsokaci kan bayyana kadarorinsu da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo suka yi a makon da ya gabata.
Shugaban Amurka Barack Obama ya fara ziyarar aiki a kasashen Kenya da Habasha inda zai tattauna huldar kasuwanci da kasashen biyu.
Masana a fannin siyasa da harkokin diplomasiyya sun fara tsokaci kan ziyarar aiki ta kwanaki uku da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kawo Amurka domin tattaunawa da takwaran aikinsa Barack Obama.
Gwamnan jahar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya, Rochas Okorocha, ya nisanta al'umar Igbo da gidan Radiyo Biafra da ake zargi da watsa labaran karya da tunzura mutane.
Rahotanni daga Jahar Gombe na cewa an gudanar da jana’izar wasu daga cikin mutanen da suka rasa rayukansu a tagwayen hare-haren da aka kai a wasu tashoshi mota da ke jahar.
Ga dukkan alamu har yanzu jam'iyar adawa ta PDP a Najeriya ba ta hakura da burinta na ganin cewa an sauya shugabar rikon kwarya hukumar zaben ta INEC Amina Zakari ba.
Mayakan IS masu da'awar kafa daular musulunci sun kai hari kan wani jirgin ruwan sojin kasar Masar da ke yankin Sinai.
Wani hari da ake zaton dakarun Amurka ne suka kai, ya yi sanadin mutuwar wasu mayakan Al Shabab su 30 a kudancin Somaliya.
Yayin da ya ke mika ragamar tafiyar da dakarun Najeriya, tsohon babban hafsan sojin kasar Laftanar Janar Kenneth Minimah ya ce kadan ya rage 'yan kungiyar Boko Haram sun kassara dakarun Najeriya.
Jam'iyar adawa ta APC a jahar Taraba na kalubalantar jam'iya mai mulki ta PDP bisa zargin nadin shugabanin rikon kwarya a kananan hukumomin jahar.
Yayin da ake samun karin hare-hare a wasu sassan Najeriya, shugabannin addinai sun yi kiran a dukufa wajen yin addu'oi domin kawo karshen matsalar Boko Haram.
Kotu a Jahar Kano ta baiwa kungiyar lauyoyi umurnin ta binciki lauyan tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wato Okechukcwu Nweze, saboda karya da ya yi a gaban kotun.
Domin Kari