Bayan rashin lafiya da ya yi fama da ita, fitaccen mawakin Hausa nan da aka fi sani da Dan Maraya Jos ya rasu.
Musulmi a Najeriya da na wasu kasashe da dama sun fara neman watan Ramadana a yau Laraba. Idan har aka ga watan, hakan na nufin watan Sha'aban ya kare ke nan, za kuma a kwashe kwanaki 29 ko 30 ana azumin.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya na Afrika ta Kudu inda ya je halartar taron koli na kasashen Afrika.
Tun bayan da ta bayyana aniyar ta sake tsayawa neman takarar shugabancin kasar Amurka, tsohuwar Sakatariyar harkokin wajen kasar, a yau Asabar Hillary Clinton ta yi wani gangami mafi girma a birnin New York.
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya ce rashin aikin yi ga matasa a kasar babbar matsala ce idan aka yi la’akkari da cewa fiye da rabin al’umar kasar matasa ne.
Bayan kwashe kusan mako guda ana takaddama a majalisar dattawan Najeriya kan zaben sanata Bukola Saraki a matsayin shugaban majalisar, jam'iyyar APC ta ce ta amince da zaben da aka mai bayan adawa da ta yi da zabensa a baya.
Sashen Hausa na VOA ya yi wata hira ta musamman da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kan batutuwan da suka shafi tattalin arzikin kasa, da tsaro da taron G7 da sauransu da tafiye-tafiyen da ya yi tare da Aliyu Mustapha.
Wani jami’in tsaron Burtaniya, ya ce sun samu rahotanni da ke nuna cewa kimanin mutane miliyan daya daga kasar Libya na shirin tsallaka tekun Meditareniya mai cike da hadari, domin samun ingantacciyar rayuwa a nahiyar Turai.
Kasashen da suka fi manyan masana’antu a duniya na G7 suna gudanar da taro a yankin Bavarian Alps da ke kasar Jamus, inda za su ci gaba da tattaunawa kan rikicin Ukraine da matsalar bashin Girka.
Shugabannin kungiyoyin fararen hula sun ce taron gangami da aka gudanar a birnin Yamai da kewaye ya yi nasara matuka.
A gobe Litinin, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, zai mika bukatun kasar a gaban taron koli na kasashen da su ka fi karfin arzikin masana’antu a duniya na G7 da ke gudana a kasar Jamus.
Dangantaka tsakanin Amurka da China na kara yin tsamari, inda a kwanan nan China ta yi watsi da sukar da Amurkan ke yi na mallake wasu filaye da Chinan ke yi a yankin Kudancin tekun kasar.
Rahotanni daga Burundi na cewa shugaban kasar Pierre Nkurunziza, ba zai halarci taron kolin shugabannin kasashen yankin gabashin Afrika ba, wanda zai tattauna kan rikicin siyasar kasarsa.
Yau Lahadi 31 ga watan Mayu, rana ce da hukumar lafiya ta duniya, WHO ta ware domin ci gaba da fadakarwa kan illar da tabar sigari ke yi ga dan adam.
Bayan da aka rantsar da gwamnoni a jahohin Najeriya, yanzu haka wasu daga sabin gwamnoni na shirye shiryen gudanar da binciken gwamntocin da suka shude, kamar yadda ya ke faruwa a jahar Kebbi.
Sabon gwamnan Jahar Filato, Barrister Simon Lalong ya yi sha alwashin ganin cewa Jahar Filato ta koma kamar yadda aka santa a da.
Bayan rantsuwar kama aiki, sabon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya ce idan har ana so a shawo kan matsalar Boko Haram, sai shelkwatar sojin kasar ta koma Maiduguri, babban birnin Jahar Borno.
Yau Juma'a 29 ga watan Mayu, Najeriya ta kafa sabon tarihi, bayan da aka rantsar da Muhammadu Buhari a matsayin sabon shugaban kasar Najeriya tare da mataimakinsa Farfesa Yemi Osibanjo.
Yayin da ake fama da matsalar kwarar bakin haure masu neman mafaka a kasashe masu galihu, hukumomin Malaysia sun ce 'yan sanda sun gano wasu manyan kaburbura cike da kasuwuwan mutane.
A birnin Cleveland na Amurka, kura ta lafa bayan da zanga zanga ta barke a lokacin da wata kotu ta wanke wani dan sanda farar fata daga zargin kisan wasu babaken fata biyu da ya auku a shekarar 2012.
Domin Kari