Ga dukkan alamu kace-nacen da ake yi a Najeriya tsakanin mai magana a madadin jam'iyyar APC da mai mulki da na jam'iyyar PDP mai adawa ya kazance
Kwamitin Sulhun na Majalisar Dinkin Duniya ya yi tir da harin da kungiyar mayakan Al-Shabab da ke Somaliya ta kai jiya Lahadi a wani otel da ke birnin Mogadishu.
Bayan da rahotanni suka nuna cewa sojoin Najeriya sun saki akalla wasu mutane 182 da a ke zargi da alaka da Boko Haram, masu sharhi kan al’amuran yau da kullum sun ce akwai bukatar gwamnati ta tallafa musu.
An sako dan kasar Ingila na karshe dake tsare a gidan kurkukun nan na Amurka dake kan tsibirin Guantanamo a kasar Cuba.
Hukumomin kasar Iran sun cakfe wani mutum wanda dan kasashe biyu ne, wato Iran din da Amurka a lokacin da ya je kai ziyara ga danginsa dake birnin Tehran.
Manyan Jami’an hukumar kula da shige da fice ta kwastom sun yi murabus daga kan mukamansu a Najeriya.
A Najeriya, gwamnatoci da dama ne suka shude, wadanda suka yi ta kokarin su kawo sauye-sauye a fannin man fetur din kasar, amma abin ya cutura.
Karancin ma’aikatan kiwon lafiya na ci gaba da janyo cikas wajen gudanar da ayyukan kula da lafiyar marasa lafiya a Jihar Niger da ke arewacin Najeriya.
Tun bayan da Kungiyar Boko Haram ta kaddamar da hare-hare a arewa maso gabashin Najeriya, dubban mutane ne suka rasa rayukansu kana wasu miliyoyi suka fice daga muhallansu.
Kungiyar Hadakar jami’yun adawa a Jamhuriyar Nijar, sun sha alwashin gudanar da wani gangami a ranar Lahadi mai zuwa domin nuna rashin jin dadinsu ka yadda ake tafiyar da shirye shiryen zaben da ke tafe.
Wani samamen da aka kai yau Litini kan wata mabuyar ISIS da ke kudu maso gabashin Turkiyya ya yi sanadin mutuwar a kalla 'yan sandan Turkiyya biyu da mayakan tara, a cigaba da kokarin da hukumomi ke yi a Siriya na wargaza tungar masu tsaurin ra'ayi da ke ketare
Wani jagoran 'yan adawa na ikirarin nasara a kuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka kada jiya Lahadi a Janhuriyar Dimokaradiyyar Congo, saboda abin da ya kira rashin fitowar jama'a sosai.
A Jahar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya, an fara ta da jijiyar wuya game da basussuka da ake zargin sabuwar gwamnatin gwamna Sanata Muhammadu Ummaru Jibrilla Bindo ke karba domin gudanar da wasu hidimomin jahar.
Yayin da gwamnatin Muhammad Buhari ke kokarin nada ministoci, kwararru na korafin cewa ana tuya ana mantawa da albasa, domin ba a tafiya da matasa.
Babban Hafsan sojin Najeriya, Manjo Janar Tukur Buratai ya jaddada cewa dakarun kasar za su cimma burinsa na dakile matsalar Boko Haram bisa lokacin da gwamnatin tarayya ta kayyade musu.
A Jamhuriyar Nijer daliban makarantun boko sun gudanar da zanga-zanga a yau litinin a titunan Yamai domin nuna bacin rai a game da abinda suka kira rashin cika alkawali akan maganar wasu bukatun da suka gabatar hukumomin ilimi.
Rahotanni daga birnin Agadez da ke kasar Jamhuriyar Nijar na nuna cewa an kama wani dan jaridar Najeriya da ye je yin bincike kan yadda ‘yan nahiyar Afrika ke bi ta kasar domin kaiwa ga kasashen turai.
Kungiyar gwamnonin juhohin Najeriya da kamfanin NNPC da ke kula da hadahadr man kasar, sun kulla wata yarjejeniyar dakile hanyoyin da ake bi wajen satan man kasar.
Rahotanni daga Jahar Taraban Najeriya na cewa an sace akalla shanun wasu Fulani guda 150 inda ake zargin al’umar Jukunawa da yin awon gaba da shanun.
Masana Najeriya na kira ga gwamnati da al’umar kasar da su koma harkar noma domin a ciyar da kasar gaba ganin cewa da kudaden noma aka gina Najeriya ta kai matsayinta na farko a idon duniya.
Domin Kari