Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wadanda Soji Suka Sake Na Bukatar Tallafi


Wasu Mutanen da aka ceto daga dajin Sambisa a wani sansani suna jira a duba lafiyarsu
Wasu Mutanen da aka ceto daga dajin Sambisa a wani sansani suna jira a duba lafiyarsu

Bayan da rahotanni suka nuna cewa sojoin Najeriya sun saki akalla wasu mutane 182 da a ke zargi da alaka da Boko Haram, masu sharhi kan al’amuran yau da kullum sun ce akwai bukatar gwamnati ta tallafa musu.

A cewar shugaban Cibiyar Horar da ‘yan majalisu a Africa, Dr Usman Danlami Muhammad, mutanen na bukatar taimako domin yawancinsu idan sun fito ba su da madogara.

“Wasansu da yawa muna jin labarin cewa suna neman ‘yan uwansu ne ko iyayensu ko mazajensu ko matansu, wasu an kashe su wasu kuma suna cikin gari sun bazama.” In ji Dr. Muhammad.

Ya kara da cewa yaki wani abu ne da ya kunshi bayan mutum ya tsira yana kuma bukatar wani tallafi na musamman domin ya dawo cikin hayyacinsa.

“Bai kamata ba a ce da an kama su a sake su, ya kamata a zauna da su a tantance su a duba hankalinsu da natsuwarsu, saboda halin ni ‘yasu da suka shiga, wasu sun ga jini wasu sun ga yadda aka kashe ‘yan uwansu.” Ya kara da cewa.

Rikicin Boko Haram a Najeriya wanda ya faro tun daga 2009, ya yi sanadin mutuwar mutane sama da dubu 12,000 kana ya raba wasu miliyoyi da gidajensu, musamman ma a arewa maso gabashin kasar.

Domin jin karin bayani saurari cikakkiyar hirar Dr. Usman Danlami Muhammad da Grace Alheri Abdu:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Shiga Kai Tsaye

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG