Gwamnatin jihar Taraba ta baiwa sabon sarkin al’uman Mumuye da ke jihar Taraba Kpanti Zing Alh. Suleiman Ibrahim sanda mai daraja ta daya a matsayin Kpanti na bakwai.
A yau Asabar, ana sa ran wakilai daga kasashen Amurka da China da Afghanistan da kuma Pakistan, za su amince da wani shirin zaman lafiya da ake kokarin shiryawa tsakanin gwamnatin Afghanistan da kungiyar Taliban a birnin Islamabad.
Wata girgizar kasa da ta afkawa garin Tainan da ke kudancin Taiwan a yau Asabar ta halaka mutane 11, bayan da ta ruguza wani babban bene. Daga cikin wadanda suka mutu har da wani jariri.
Hukumomi a Brazil sun ce an samu burbushi ko kuma samfurin kwayar cutar Zika a yawu da kuma fitsarin masu dauke da cutar.
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta musanta zargin da ‘yan adawa ke yi na cewa shugaba Issoufou Muhammadou na amfani da sarakuna wajen yin kamfe domin ta lashe zabe mai zuwa.
Rahotanni daga jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa wasu da ake zargi ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun kai wani mummunan hari a jihar.
Kwamitin da ke binciken rikicin 'yan Shi'a da sojojin Najeriya da gwamnatin jihar Kaduna ta kafa, ya ba da tabbacin cewa zai yi adalci a ayyukansa amma kuma ya ce yana bukatar hadin kan jama'a.
Kungiyar Nakassun jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya, ta gudanar da taron addu’oi ga kasar domin neman Allah ya kawo karshen matsalar hare-haren da ke addabar kasar
Takaddama tsakanin kwamitin katta-kwana na gwamnatin jihar Kano kan sha’anin albarkatun man fetur da kungiyar dillalan man da kuma takwararta ta masu motocin dakon albarkatun mai ta barke a jihar.
Wasu jerin hare-haren bam, sun kashe akalla mutane 45 a birnin Damascus da ke Syria a yau Lahadi.
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, ya yi kira ga shugabannin kasashen Afirka, inda ya ce bai kamata a rinka nuna jinkiri ba wajen kokarin shawo kan rikicin kasar Burundi domin mutane na ci gaba da mutuwa.
Ana ci gaba da neman wasu mutane takwas bayan da wani jirgin ruwa na fasinja ya kife ya halaka wasu daga cikin fasinjojin da ke ciki.
Ana ta suka tare da yaba matakin soke zabuka da kotun koli ta dauka kan zabukan wasu sanatoci biyu daga jihar Anambra.
An kaddamar da yakin neman zabe a Jamhuriyar Nijar tun daga karfe 12 daren jiya Juma’a domin a baiwa ‘yan takara baje kolinsu ga masu kada kuri’a.
Bayan kwashe kusan shekaru biyar ana yaki basasa a kasar Syria, ana shirin wani zaman sasanta rikicin kasar a birnin Geneva, taron da ake fargabar bangaren masu shiga tsakani da Saudiya ke marawa baya ba za su halarta ba.
An bude taron kolin kasashen Afrika a kasar Habasha domin tattauna matsalolin da ke fuskantar nahiyar.
Wani dan Majalisar dattawa a Najeriya, ya yi kira ga tsohon shugaban kasar, Olusegun Obasanjo, da ya ba da hujja tare da bayyasan sunyen wadanda ya zarga da yin sama da fadi da wasu kudaden da aka ware musu domin mazabunsu.
Litinin cewa 'yan sanda sun damke wasu mutane 16 da ake zargin 'yan ta'adda ne a Brussels, babban birnin kasar, amma har yanzu ba a kama Salah Abdulsalam ba, mutumin da ake fi zargi dangane da kashe-kashen da aka yi a Paris
Matasa a tsibirin Gobir da ke Jihar Maradi, sun yi ta kone-kone bayan da suka ji jita-jitar za a sanya shingayen binciken ‘yan sanda tsakanin birnin Maradi da tsibirin.
Akalla mutane uku ne suka rasa rayukansu cikinsu har da wata ‘yar jaririya ‘yar kasa da shekara daya da rabi bayan da wata doguwar mota makare da shanu ta fadi akan wasu motoci biyu.
Domin Kari