Hukumomin Nijar sun ce za su karbe kasha 50 cikin dari na yawan man da ake hakowa daga hanun kamfanin Sonidep ta maida shi zuwa hanun kamfanin matatar man ta Soraz.
A jihar Taraba ana cigaba da cecekuce dangane da rashin gudanar da kananan hukumomin. Fiye da shekara guda Kenan da nada shugabannin rikon kwarya ko kuma kantomomi a kananan hukumomi 16 da ke jihar.
Jami’ai a Indonesisa sun ce akalla mutane shida ne suka mutu, bayan aman toka mai tiriri da wani dutse ya yi.
Shugaban Masar, Abdul Fattah al Sisi, ya gargadi kafafen yada labarai da su guji yin shaci-fadi, kan abin da ya haddasa hadarin jirgin saman Egypt Air mai lamba 804, yana mai cewa ana kan duba kowane fannin abin da ka iya haifar da hadarin.
Hukumar leken asiri ta Afghanistan, NDS, ta ba da tabbacin mutuwar shugaban kungiyar Taliban Mulla Akthar Mansoor.
Uwargidan tsohon shugaban Najeriya Hajiya Turai ‘Yar’adua, ta musanta rahotanni da ke nuna cewa ta ce an manta da su bayan mutuwar mai gidanta.
Dakarun Najeriya sun ce kowane dan Najeriya daidai ya ke a idonsu ba sa nuna fifiko akan kowa a ayyukan da su ke yi na samar da zaman lafiya a arewa maso gabashin kasar.
Bayan da aka kammala taron gangami na babbar jam’iyar adawa ta PDP a birnin Fatakwal da ke jihar Rivers a Najeriya, har yanzu ana cigaba da takaddama kan waye shugaban jam’iyar a yanzu.
Adadin mutanen da suka mutu bayan da Wata guguwa mai karfi da akawa lakabi da “Roanu”, ta ratsa ta gabar tekun kasar Bangladesh a yau Asabar,na cigaba da karuwa.
Rahotanni daga Najeriya na cewa babbar jam’iyar adawa ta PDP kasar ta zabi tsohon gwamnan jihar Kaduna Sanata Ahmed Makarfi a matsayin shugabanta na rikon kwarya.
Hukumar da ke kula da yaduwar kananan makamai ta kasar Ghana, na shirin kaddamar da wani tsari da zai wayar da kan al’umar kasar ta kafafen yada labarai, ta yadda za su farga.
Bayanai na nuni da cewa, mintina kadan kafin jirgin saman kasar Masar na Egypt Air mai lamba 804 ya fada cikin teku ranar Alhamis, an samu sakon da ke nuna cewa akwai damuwa a cikin jirgin.
Shugabannin ‘yan kasuwa a Jamhuriyar Nijar sun yi ittifakin cewa ba za su kara farashin kayan masarufi ba, yayin da ake shirin tunkarar azumin watan Ramadana
Babbar Jam’iyar adawa ta PDP a Najeriya ta soke gudanar da babban taronta da ta shirya gudanarwa a birnin fatakwal da ke jihar Rivers a yau Asabar.
Rasha ta ce ta ji takaicin kin amincewa da aka yi da kudirin da ta gabatarwa Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya nemi Turkiyya ta kawo karshen ayyukan sojinta a Syria.
A yau Asabar Firai ministan Burtaniya David Cameron ya bayyana cewa a ranar 23 na watan Yuni mai zuwa, za a yi zaben raba gardama kan ci gaba da kasancewar kasar a kungiyar tarayyar turai ta EU ko kuma akasin hakan.
Ranar 21 ga watan Fabrariru, rana ce da ‘yan Jamhuriyar Nijar za su garzaya zuwa rumfunan zabe domin zaben shugaban kas ada na ‘yan majalisun dokoki.
Hukumar zabe ta CENI a Jamhuriyar Nijar ta ba da tabbacin cewa kayayyin zabe za su isa rumfuna zaben akan kari da sassa dabdan daban na kasar.
Shugaban kasar Uganda Yuweri Musveni ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi, bayan da ya samu kashi kusan 61 na kuri’un da aka kada.
Zaben kananan hukumomi a Najeriya kan zo a lokuta daban daban a juhohin kasar, inda akan samu gwamnoni ke nada kantomomi gabanin a yi zabe.
Domin Kari