Yayin da ake cigaba da azumtar watan Ramadana a duk fadin duniya, a Najeriya magidanta na korafi kan yadda ake samun hauhawan farashin kayan masarufi.
Rahotanni daga Najeriya na cewa tsohon kocin ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles, Stephen Keshi ya rasu. Ya rasu yana mai shekaru 54.
Musulmi a duk fadin duniya na shirin fara azumin wata mai tsarki na Ramadana, wanda ake sa ran zai fara a ranar Litinin, bisa ga yadda aka ga jinjirin wata.
Ana ci gaba da shirye shiryen gudanar da jana’izar zakaran dan damben zamani na Amurka, Muhammad Ali, wanda da ya rasu cikin daren juma’a, yana mai shekaru 74, bayan da ya sha fama da cutar Parkinson mai sa kakkarwa.
Sakataren harokokin wajen Amurka, John Kerry, ya isa birnin Beijin bayan da ya kai wata ziyara a Mongolia, ziyarar da ta sha banban da irin wadanda ya ke kaiwa, wacce kuma ita ce ta farko da ya kai a matsayinsa na babban jami’in Amurka.
‘Yan kasar Jamhuriyar Nijar sun nuna kaduwa da asarar rayukan sojojin kasar kimanin 30 bayan kazamin harin da kungiyar Boko Haram ta kai a yammacin juma’ar da ta gabata a garin Boso dake yankin Diffa.
Rahotanni daga jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa har yanzu ana ci gaba da samun rashin jituwa a tsakanin ‘ya’yan jam’iya mai mulki ta APC a jihar.
Akalla mutane 12 aka tabbatar da mutuwarsu bayan wani hadarin mota da ya uku a cikin birnin Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya.
Hukumomin Najeriya sun ce ya zuwa yanzu sun kwato sama da naira biliyan 78 daga hanun tsoffin jami’an gwamnati da ‘yan siyasa a cigaba da yaki da gwamnatin Muhammadu Buhari ke yi da cin hanci da rashawa.
Wani hari da aka kai barikin soji da ke Boso a yankin Diffa na Jamhuriyar Nijar, ya yi sanadin mutuwar sojoji 34, bayan da wasu mahara da ake tunanin ‘yan Boko Haram ne suka kai hari a sansanin soji.
Fitattun 'yan wasa na cigaba da aikawa da sakkonin ta’aziyya da nuna alhini daga sassan daban daban na duniya, dangane da rasuwar shahararren tsohon dan wasan damben zamanin Amurka Muhammad Ali, wanda ya rasu a daren jiya Juma'a a wani asibiti da ke Phoenix a jihar Arizona.
Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na cewa sojojin kasar sun yi wata arangama da wasu mayakan Boko Haram da suka fada cikin barikin sojin Boso.
Fiye da bakin haure 700 ne ake fargabar sun nutse a ruwa a wannan makon a wasu kwale-kwale guda uku, yayin da suke kokarin ketara tekun bahrurrum domin kaiwa ga nahiyar turai, a cewar hukumar da ke kula da ‘yan gudun hijra ta Majalisar Dinkin Duniya.
Ruwan sama da aka aka yi ta tafkawa kamar da bakin kwarya, wanda da ya haifar da ambaliyar ruwa a ‘yan kwanakin nan a jihar Texas da ke kudancin Amurka, ya halaka mutane hudu, a cewar jami’an ba da agajin gaggawa.
Bangaren Majalisar Dokokin Najeriya, wani bangaren ne shima da ke shirin cika shekara guda da kafuwa, wato a jamhuriyar ta takwas.
A ranar mai kamar ta yau, wato 29 ga watan Mayun shekarar 2015, aka rantsar da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a karkashin jam’iyar APC, bayan da ya doke abokin hamayyarsa Goodluck Jonathan na jam’iyar PDP.
Matsalar tsaro na daya daga cikin batutu8wan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi alkawarin zai magance, musamman a yankin arewa maso gabashin aasar da ke fama da matsalar Boko Haram.
Rahotanni daga birnin Maiduguri da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya, sun ce wasu mutane hudu sun rasa rayukansu, bayn da wasu ‘yan kunar bakin wake suka kai hari a wata unguwa mai suna Sajeri.
Kusan masu zanga zanga dubu ne suka yi dandazo tare da raira waka a wajen wani babban dakin taro da ke San Diego, yayin da Donald Trump da ake tunanin zai yiwa jam’iyar Republican takarar shugabancin Amurka, ya ke jawabi ga magoya bayansa.
Duk da cewa kwamitin amintattun babbar jam’iyar adawa ta PDP a Najeriya ya kira wani zama domin neman bakin zaren rikicin shugabanci da ya barke a jam’iyar, har yanzu ba a yi kusa da kawo karshen takaddamar ba.
Domin Kari