Bayan da aka kammala manyan turakan jam’iyyun siyasa a Amurka, yanzu hankula za su karkata ne akan ‘yan takarar da jami’yyun suka fitar, wato Donald Trump a karkashin jam’iyyar Republican da kuma Hillary Clinton a bangaren jam’iyyar Democrat.
Mutanen da ba a san adadinsu ba sun samu raunuka bayan da ‘yan sandan Jamus suka ce an yi harbe-harbe a wasu shaguna cinikayya, lamarin da ya sa jami’an tsaro suka yi tururwa zuwan wurin.
Kwana guda bayan da dan takarar jam’iyar Republican, Donald Trump, ya sha alwashin gina Katanga tsakanin Amurka da Mexico, shugaban kasar Mexicon, Enrique Pena Nieto, na ziyara a Amurkan a yau Juma’a.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa na tattaunawa da kungiyar tsegerun Niger Delta Avengers domin ganin yadda za a kawo karshen hare-haren da su ke kaiwa akan bututai da kayayyakin mai.
Yayin da ake shirin kammala taron da ke dubi kan inda ake a yakin da ake yi cutar kanjamau ko kuma AIDS/SIDA a birnin Durban na Afrika ta Kudu a yau Juma’a, masana na shakkun ko za a iya shawo kan cutar nan da shekarar 2030.
Bayan kwashe wani lokacin mai tsawo ana takaddama dangane da batun sanya hijabi a makarantun jihar Legas, wata kotu ta yanke hukuncin cewa dalibai mata musulmi za su iya saka hijabi a makarantun.
Firai Ministan Turkiyya, Binali Yildrim, ya ce akwai yiwuwar ana shirin yin juyin mulki a Ankara, lamarin da ya kwatanta a matsayin abinda ya sabawa doka.
Kusan za a iya cewa tun bayan da aka kafa wannan majalisar dokokin Najeriya a jiko na takwas, majalisar mai zauruka biyu ta ke fama da takaddama iri-iri.
Mutumin da ake ganin shi jam’iyar Republican za ta tsayar dan takarar shugaban kasa a Amurka, Donald Trump, ya zabi gwamnan Indiana, Mike Pence a matsayin abokin takararsa.
Hukumar Amurka mai kula da raya kasashe domin samar da ci gaba ta USAID tare da hadin gwiwar hukumar binciken sararin samaniya NASA sun kaddamar da wani shiri na musamman da ake kira SERVIR.
Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar dinkin Duniya UNICEF, ya ce daga cikin yara miliyan 10 da bas a zuwa makaranta, fiye da miliyan uku daga cikinsu yara ne masu fama da nakasa.
15 ga watan Yulin kowace shekara, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin bita da nuna muhimmancin koyawa matasa dogaro da kai.
Ma’aikatun harkokin wajen kasashe da dama na ci gaba da bayyana ‘yan kasarsu da suka rasu a harin da aka kai a garin Nice da ke Faransa a jiya Alhamis.
A Najeriya rundunar jami’an tsaro na farar hula NSCDC da ke jihar Borno, ta ce ta gano wani littafi ko kuma kundi da mayakan Boko Haram ke amfani da shi wajen sauya tunanin mabiyansu musamman masu zuwa kai harin kunar bakin wake.
Yau shirin babban bankin Najeriya na farfado da darajar naira zai fara aiki bayan da hukumomi suka bayyana a makon da ya gabata cewa za su cire hannunsu a hadahadar cinikayar canjin kudaden kasashen waje.
Ranar 20 ga watan Yuni, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin duba halin da ‘yan gudun hijra ke ciki, wadanda suka bar muhallansu a sassa daban daban na duniya.
A nan Amurka, an harbe wata mawakiya har lahira, wacce ta lashe gasar waka da gidan talbijin na NBC ke shiryawa.
Mayakan Al Shabab a Somalia, sun ce sun kashe wasu mambobinsu biyu, wadanda suka shiga kungiyar daga Kenya, saboda kin bin umurni da kuma sabawa koyarwar addinin Islama.
Tsohon mai horar da ‘yan wasan Super Eagles na Najeriya, Shu'aibu Amodu ya rasu. Ya rasu yana mai shekaru 58.
Rahotanni daga Najeriya na cewa rundunar tsaron kasar, ta yiwa wasu manyan sojojin kasar ritaya.
Domin Kari