Gwamnatin kasar Uzbekistan ta fitar da wata sanarwa da ke tabbatar da cewa shugaban kasar na fama da rashin lafiya mai tsanani.
Uwargidan dan takarar shugaban kasa na Republican Donald Trump, Melinia Trump ta kai ma’aikatar jarida ta Daily Mail Online kotu akan labarin da ya yi cewa ta yi aikin karuwanci a cikin shekarun 1990 a birnin New York.
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya jinjinawa shugaban kamfanin shafin sada zumunta na Facebook, Mark Elliot Zuckerberg, saboda karawa matasa ilimi da ya yi wajen fadada fahimtarsu da dabarunsu kasuwanci
A Jamhuriyar Nijar kungiyar lauyoyi da hukumar UNHCR mai kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, sun cimma wata yarjejeniya domin samar da kariyar da ta dace ga ‘yan gudun hijira da masu neman mafakar siyasa, abinda masu fafukar kare hakkin dan adam su ka ce ya yi dai dai.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ba da umurnin gudanar da bincike, domin gano wadanda ke karkata akalar kayan abincin da ake aikawa masu gudun hijra a jihar Borno.
Gwamnatin Jihar Filato ta fara share fagen kaddamar da shirin ba da takardun iznin mallakar filaye, inda ta gayyaci jama’a domin su ba da na su shawarwari kan yadda za a gudanar da aikin domin kaucewa fuskantar matsaloli.
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka, ta gargadi ‘yan kasar ta da su guji zuwa yankunan arewa mai nisa a kasar kamaru, saboda masu garkuwa da mutane da ‘yan ta’adda da ke kai harin kunar bakin wake.
Wani faifan bidiyo da ya nuna wani karamin yaro a Syria jina-jina bayan hare-haren da jiragen sama su ka kai a Aleppo, ya ja hankula jama'a a duniya. Hoton dai ya karade shafukan sada zumunta musamman a kafar Youtube.
‘Yan jami’iyar Republican ta nan Amurka suna sukar lamirin gwamnatin shugaba Obama akan wani labari da ya fito Alhamis cewa Amurka ta kashe dala miliyon 400 wurin karbo wasu Amurkawa ‘yan fursuna dake zaman gidan yari a Tehran.
Wani mutum a Yola da ke jihar Adamawa a arwea maso gabashin Najeriya, ya tsinci kansa a wani mawuyacin hali, bayan da wani likita ya cire mai kodoinsa yayin da ya je da kuken ya na fama da ciwon ciki.
A duk fadin duniya, ba kasafai ne gwamnati ke barin ma'aikatanta su shiga wata harka ba, musamman wacce za ta iya karo ko kawo cikas ga aikin da mutum ke gudanarwa.
19 ga watan Agusta, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin tunawa da masu ayyukan jin kai da suka rasa rayukansu a fagen yaki ko kuma yayin da su ke ba da taimako wuraren da bala’i ya abkawa.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyar Republican Donald Trump, ya fada a yau juma'a cewa batun da ya yi na cewa shugaba Obama ne ya kafa kungiyar ta’addanci ta IS, ba’a kawai ya ke yi.
Rahotanni daga Najeriya na cewa hukumomin kasar sun taru jami'an kiwon lafiya zuwa jihar Borno bayan da aka samu bullar cutar polio a jihar.
Wani babban jami’in tsaro a Angola, Kanar Silvano Ndogua, ya zargi gamayyar ‘yan adawa da su ka yi zanga zanga da laifin ta da tarzomar da ta kai ga wasu sojoji su ka harbe wani matashi har lahira a babban birnin kasar a makon da ya gabata, da kuma wasu masu rusau da suka yi sanadin mutuwar wani jariri.
Ana sa ran Michael Phelps da Katie Ledecky da ke jagorantar ‘yan wasan Amurka a gasar wasannin Olympics, za su ci gaba da nuna bajintarsu a yau Juma’a, inda suka mallake mafi yawan kyautar zinare a bangaren masu ninkaya.
12 ga watan Agusta, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin yin dubi kan irin halin da matasa ke ciki.
Uwargidan shugaban Najeriya, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari, ta ce ‘yan gudun hijra da rikicin Boko Haram ya tilastawa ficewa daga gidajensu a arewa maso gabashi kasar na bukatar taimakon gaggawa.
Yankin Arewa maso gabashin Najeriya, yanki ne da ya sha fama da hare-haren ‘yan kungiyar Boko Haram wadanda suka halaka sama da mutane 20,000 kana wasu miliyoyi suka arce daga gidajensu cikin shekaru kusan bakwai da suka gabata.
Sarwat Husain ta san cewa hijabin da ta kan saka, a wasu lokuta ya kan ja hankulan jama'a a jihar ta Texas. Amma kallon da wani mutum ya mata, yayin da ta ke cikin jirgi akan hanyarta ta zuwa birnin Orlondo na jihar Florida, ya fita daban
Domin Kari