A yau Lahadi, jam’iyar masu ra’ayin mazan jiya, na gudanar da zaben fidda gwanin wanda za su tsayar takarar shugaban kasa a Faransa, bayan yakin neman zaben da aka gina kan kyamar baki da ake zargin suna tururuwa zuwa nahiyar Turai, da kuma hare-haren ta’addanci da ake kaiwa a Faransan.