‘Yan kabilar Igbo dake zaune a jihar Naijan Najeriya, sun bi sahun takwarorinsu dake zaune a wasu yankunan Arewacin kasar wajen yin watsi da gwagwarmayar da wasu ‘yan kabilar su ke yi ta neman kafa kasar Biafra.
A karshen watan da ya gabata jami’an tsaro suka kama Gamaci Muhammad na kawancen kungiyoyin masu fafituka, bayan da aka zareg shi da shiga shafin Facebook ya muzanta wasu alkalan kasar, lamarin da ya sa hukumomi suka tsare shi.
Matsalar tsaro akan iyakokin Najeriya da Nijar musamman ta fuskar dakile masu safarar makamai, na daga cikin matsalolin dake ci wa hukumomi tuwo a kwarya. Amma rahotannin daga Jamhuriyar ta Nijar na nuni da cewa a 'yan kwanakin nan jami’an tsaron kasar na samun galaba akan 'yan fashi da masu aikata miyagun laifuka.
Rahotanni daga kungiyoyin cikin gida da na waje, sun sha bayyana korafinsu kan yadda ake samun tsaiko da kin aiwatar da kasafin kudade da gwamnatoci ke gabatarwa a matakn daban-daban.
Bayan da Jam’iyar PDP mai adawa ta lashe zaben sanata a mazabar Osun ta yamma dake jihar Osun a kudu maso yammcin Najeriya, masu fashin baki a fannin siyasa na ganin sakamakon zaben tamkar zakaran gwajin-dafi ne ga zabuka dake tafe ga jam’iya mai mulki ta APC, lamarin da su ke ganin ya jefa fargaba a zukatan mabiyanta.
Rikicin da ya barke a karamar hukumar Sardauna a yankin Mambila na Jihar Taraba tsakanin Fulani da kabilar yankin a Najeriya, ya haifar da dubban 'yan gudun hijira wadanda da yawansu ke makale a wasu kauyuka dake kasar Kamaru mai makwabtaka da Najeriyar.
A karon farko tun bayan da ya karbi ragamar mulkin Amurka, shugaba Donald Trump ya gana da takwaran aikinsa na Rasha, Vladimir Putin, tattaunawar da ta mamaye taron kasashen G20 masu karfin tattalin arziki a duniya dake gudana a Jamus.
Ana ci gaba da samun bayanai masu ingancin kan yadda wasu 'ya'yan kungiyar Boko Haram su 70 suka gujewa sansaninsu suka ajiye makamansu tare da mika wuya a garin Maiduguri dake jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.
Kowace ranar 4 ga watan Yuli, rana ce da Amurkawa kan ware domin yin shagugulan tunawa da zagayowar ranar da kasar ta samun 'yancin kai daga Burtaniya. Akan ba da hutu a duk fadin kasar domin mutane su samu damar yin bukukuwa.
rahotanni daga kasar Ghana na cewa akalla mutane 14 ne suka makale a wani ramin hakar ma'adinai bayan da ramin da suke aiki a cikinsa ya rufa, lamarin da ya sa masu ayyukan ceto ke kokarin kubutar da mutanen.
Zargin cewa hamshakin mai kudin nan da ya fi kowa arziki a nahiyar Afrika wato Aliko Dangote, ya ba da wasu miliyoyin kudade domin a yi watsi da binciken da majalisar ta sa a gaba kan masarautar Kano ya bar baya da kura.
Yau Litinin wa'adin da kasar Saudiya da wasu kawayenta suka bai wa kasar Qatar kan ta cika wasu sharudda da za ta ba su damar dawo da huldar diplomasiyya da ita zai cika, bayan da Qatar din ta nemi a kara mata tsawon wa'adin.
Yayin da ake ci gaba da kai ruwa rana kan batun makomar Najeriya tun bayan da takaddama tsakanin masu rajin neman kasar Biafra da kungiyar matasan arewa da suka ba kabilar Igbo wa'adin ficewa daga arewacin kasar, tsohon shugaban Najeriya a lokacin mulkin soji, Ibrahim Badamasi Babangida ya ce lokaci ya yi da za a sauya fasalin Najeriya.
A karon farko kotun kolin Amurka ta ce, za a iya fara aiwatar da wani sashe na umurnin da shugaba Donald Trump ya bayar kan hana wasu 'yan kasashe mafiya rinjayen Musulmi shiga Amurkan na dan wani tsawon lokaci, ko da yake kotun ta ce akwai mutanen da wannan lamari ba zai shafa ba.
Shugabannin kungiyar Tarayyar Turai sun fara wani taron koli na kwanaki biyu a Brussels yau Alhamis don tattaunawa akan duk abubuwan da suka shafi nahiyar ta su - kama daga shirin Burtaniya na fita daga kungiyar kasashen zuwa batun hanyoyin ta da komadar tattalin arzikin kasashen yankin.
Wasu mazauna karkara a yankin Damagaram dake Jamhuriyar Nijar da aka karbi gonakinsu aka gina matatar mai ta Soraz shekaru biyu da suka gabata, na neman a biya su sauran kudadensu da ba a cika musu ba.
A duk fadin duniya, a yau ake bikin tunawa da halin da ‘yan gudun hijra ke ciki tare da yin dubi kan kalubalen da suke fuskanta da jajircewa da suke nunawa, musamman ma wadanda rikici ya raba da muhallansu.
Bayan rikicin kabilancin da ya barke a yankin Mambila dake jihar Taraba rundunar ‘yan sandan jihar ta ce yanzu hankula sun kwanta.
Domin Kari