Rikicin da ya barke a yankin Charlottesville wanda ya yi sanadiyar mutum guda a jihar Virginia da ke Amurka, na ci gaba da haifar da ce-ce-ku-ce bayan da masu nuna fifikon fatar fata da masu adawa da su suka yi arangama a karshen makon da ya gabata.
A Jamhuriyar Nijar, manajojin tashoshin rediyo da na talbijin masu zaman kansu, sun fara nuna damuwa akan wani abinda suka kira shirin rufe tashoshinsu bayan da hukumar sadarwa ta soma duba hanyoyin karbe mitocin watsa shirye-shiryensu kan cewa sun saba yarjejeniyar da ke tsakaninta da su.
Wata babbar matsala da ke addabar matasan kasashen da ke tasowa irinsu Najeriya ita ce ta rashin aikin yi, matsalar da kan jefa su cikin mawuyacin hali. Dalilin hakan, da ma wasu matsalolin Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 13 ga watan Agusta domin yin dubi kan samar wa matasan kyakkyawar makoma.
A wani mataki na ganin an magance matsalolin da masu manyan motoci suke haifarwa, kama daga bata hanyoyi zuwa haifar da hadurra a duk fadin Najeriya, hukumomin kasar na shirin samar da wuraren dakatarwar motocin a sassan kasar.
Bayan zafafan kalaman da shugaban Amurka ya furta akan Korea ta arewa dangane da barazanar da take yi wa kasarsa, Korea ta arewan ta yi wancakali da kalaman na Donald Trump inda ta ce ba zai iya aiwatar da abinda ya fada ba.
Shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta ya dauki hanyar yin tazarce a zaben kasar da aka gudanar, yayin da abokin hamayyarsa ke ikrarin an tafka magudi a zaben wanda aka yi a ranar Talata.
Lauyoyi da kungiyoyin rajin yaki da rashawa da tabbatar da shugabanci na gari a Najeriya na ci gaba da tsokaci dangane da kudaden basussuka da hukumar EFCC ta ce ta kwato fiye da naira biliyan 328 daga hannun manyan kamfanonin dillancin mai.
Wani sabon sakamakon binciken jin ra’ayin Amurkawa da aka yi kan yanayin kamun ludayin shugaba Donald Trump ya nuna cewa farin jinin Trump na kara raguwa.
Shugaban Amurka Donald Trump na kokarin soke shirin tambola na "Lottery" da kuma tsaurara matakan samun katin zama a kasar na dindindin wato Green Card, a wani kudurin dokar da yake so ya gabatarwa majalisar dokokin kasar.
Majalisar dokokin Jamhuriyar Nijar ta kudiri aniyar ladabatar da ‘yan majalisar da ba sa halartar zauran majalisar a-kai-a-kai ba tare da wata kwakkwarar hujja ba, ta hanyar rage masu albashi, sai dai ‘yan adawa sun ce akwai lauje a cikin wannan nadi.
An gudanar da taro tsakanin gwamnatin Najeriya da kungiyoyin masu fafutukar kare hakkin yara daga kasashen waje da sauran masu ruwa da tsaki akan batun cin zarafin yara da a halin yanzu ya ke nema ya zama ruwan dare a Najeriyar.
An Fara jigilar maniyyata hajjin Najeriya zuwa kasar Saudiya domin gudanar da aikin hajjin bana. An bude aikin jigilar ne da alhazan Abuja, babban birnin kasar.
Rasha ta ce za ta kori jami'an diplomasiyar Amurka kusan 800 da ke aiki a kasar a matsayin martani kan sabbin takunkumi da Amurkan ta kakaba mata.
A karo na biyu majalisar dokokin Jamhuriyar Nijar, ta yi wa wasu dokokin zaben kasar garanbawul, a wani zama da 'yan adawa suka kauracewa zauren majalisar.
Gwamnonin arewacin Najeriya sun nemi takwarorinsu na kudu maso gabashin Najeriya da su ja kunnen matasan yankunansu da ke kalamai masu haifar da rarrabuwar kawuna a Najeriya, musamman ma shugaban kungiyar IPOB Nnamdi Kanu.
Kai ruwa rana da ake yi tsakanin shugaba Donald Trump na Amurka da babban lauyan gwamnatin kasar Jeff Sessions na kara ta'azzara yayin da Sessions din ya ce ba shi da niyyar yin murabus.
Ana kara samun bayanai kan halin da shugaban Najeriya ke ciki tun bayan da ya tafi jinya a birnin London a watan Mayu, a baya-bayan nan wasu gwamnonin kasar ne suka kai mai ziyara inda suka ce sun sami shugaban cikin yanayi mai kyau.
‘Yan majalisar dokoki daga kasashe hudu na yammacin Afirka sun gudanar da taro a karshen makon da ya gabata a birnin Abidjan na kasar Ivory Coast tare da halartar wasu takwarorinsu na Jamus don tantaunawa akan matsalolin da ke haddasa ayyukan ta’addanci a nafiyar Afirka.
Majalisar dattawan Najeriya ta yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyara, kadan daga cikin abubuwan da aka yi wa kwaskwarima, akwai dokar da ta ba matasa damar tsayawa takara a matakai daban-daban ciki har da na mukamin shugaban kasa.
Rahotanni daga Maiduguri da ke Jihar Bornon Najeriya na cewa an yi nasarar kubutar da ma’aikatan matatar man fetur din kasar na NNPC bayan da wasu da ake zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne suka yi masu kwanton-bauna tare da sojojin Najeriya da ke masu rakiya a kan hanyar Magumeri da Gubio.
Domin Kari