Yayin da kasashen duniya suka kasa kunnuwansu domin jin jawabin jagorar kasar Myanmar, Aung San Suu Kyi ta gabatar da jawabin nata a karon farko kan rikicin da ya tilastawa dubun dubatar Musulmi 'yan kabilar Rohingya ficewa daga kasar.
A Najeriya sojojin kasar da dama na jibge a wasu yankuna domin gudanar da sintiri da atisaye, musamman domin kwantar da hankulan jama'a da kuma wanzar da zaman lafiya. Shin mene ne tasirin irin wannan sintiri?
Bayan shafe sama da wata guda tana yajin aiki, kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ta ASUU ta umurci malaman da su koma bakin aikinsu a yau Talata bayan wata matsaya da aka cimma da gwamnati.
Jagorar kasar Myanmar, Aung San Suu Kyi, ta jingine zuwanta babban taron Majalisar Dinkin Duniya da ke gudana a Amurka, inda ake sa ran za ta yi wani jawabi kan rikicin Rakhine da ya tilastawa dubun dubatar 'yan kabilar Rohingya ficewa daga kasar.
Wani shirin mayar da 'yan gudun hijirar kasar Burundu zuwa kasashensu na asali daga kasar Congo ya yi sanadin mutuwar sama da mutane 30.
A yini na biyu a jere, masu zanga zanga sun yi tattaki a birnin St Louis da ke jihar Missouri da ke Amurka a jiya Asabar, bayan da wata kotu ta wanke wani dan sanda farar fata da aka tuhuma da kisan wani bakar fata.
Shugabannin duniya na shirin taruwa a birnin New York da ke Amurka, domin halartar babban taron Majalisar Dinkin Duniya, inda ake sa ran batun gwajin makamin nukiliyan Korea ta Arewa shi zai mamaye batutuwan da za a tattauna a kai.
Ana zanga zanga a Amurka bayan da wata kotu ta wanke wani tsohon dan sanda farar fata daga zargin kisan wani bakar fata a St. Louis da ke jihar Missouri.
Wani harin da jami'an tsaro suka ayyana a matsayin na ta'addanci ne da aka kai a Burtaniya, ya sa hukumomin kasar sun tashi tsaye wajen tunkarar kalubalen hare-haren ta'addancin.
Wasu manyan jami’an gwamnatin Amurka biyu, sun ce shugaba Donald Trump, zai mika bukatar a kara tsaurara takunkumin tattalin arziki akan Korea ta Arewa, a babban taron Majalisar Dinkin Duniya da za a yi a mako mai zuwa.
Ana ci gaba da yin Allah wadai da rikicin Burma da ya ki ci ya ki cinyewa, inda rahotannin ke zargin cewa ana aikata kisan kare dangi akan tsurarun Musulmi 'yan kabilar Rohingya.
Wasu hare-hare da aka kai daban-daban, sun sanadiyar mutuwar mutane 16 a Somalia, harin da ake zargin kungiyar Al Shebab ce ta kitsa shi.
Mazauna tsibirin da ke kudancin Florida inda mahaukaciyar guguwar nan ta Irma ta yi wa mummunar illa, yanzu haka ba za su iya dawo wa gidajen su ba har na tsawon makonni, kamar yadda fadar shugaban Amurka ta White House ta fada jiya Litinin.
Bayan daukan wani lokaci yana shiry-shirye, Kwamitin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kafa domin ya binciki zargin da ake wa sojojin kasar na take hakkin bil'adama ya fara aiki.
Hukumar kwastam ta ce ta kama makamai sama da 2000 cikin kasa watannin tara yayin da ake kokarin shiga da su cikin Najeriya daga kasashen waje.
Masu gwagwarmayar 'yan kabilar Rohingya sun nemi a tsagaita wuta a rikicin da ake fama da shi a jihar Rakhine dake kasar Myanmar.
An yi babban wasan kwallon kafa na farko cikin shekaru 30 a Mogadishu babban birnin kasar Somalia, wasan da ya samu halartar dubban masu kallo ya kuma zama tarihi.
Guguwar Irma hade da ruwan sama ta fara dosan gabar tekun jihar Florida yayin da hukumomi ke ci gaba da kiran mutane su fice daga yankunan da aka shata guguwar za ta ratsa.
A Najeriya ana ci gaba da Allah wadai da harin da aka kai kauyen Ancha na jihar Filato, inda mutane 19 suka rasa rayukansu. A baya-bayan shugaban kasar Muhammadu Buhari ne ya yi tir da wannan hari.
A ranar Lahadin nan mai zuwa ake sa ran guguwar Irma za ta sauka a jihar Florida da ke Amurka, bayan da ta yi kaca-kaca da wasu yankunan Caribbea, inda har ta kashe mutane 22.
Domin Kari