Masu sharhi na cigaba da tofa albarkacin bakin su game da ziyarar da shugaban majalisar dattawa ya kaiwa tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida. Idan suke cewa ya kamata Majalisa da Bangaren zartawa su gyara zaman doya da manaja da suke yi
Yayin da 'yan siyasa a tarayyar Najeriya ke ci gaba da neman lasisin tsayawa takarar shugabanci, jam'iyyar APC a jihar Zamfara ta haramtawa wasu mata uku tsayawa takara.
Bayan fiye da shekaru 30 da gwamnatin jihar Kano ta mallaka gonakan wasu al’umomin kimanin kauyuka bakwai ga jami’ar Bayero, yanzu haka wasu daga cikin al’umomin na ikirarin diyyar gonakai daga mahukuntan Jami’ar.
Ya zuwa yanzu dai ‘ya yan jam’iyyar APC mai mulki a Najeriye, na ci gaba bayyana ra’ayin su game da amincewar da jami'iyyar ta yi na zaben 'yar tinke a zaben shugaban kasa.
Jami’ar tarayya dake Dutse a jihar Jigawa, ta yi wani yunkuri na kawo sauyi da farfado sana’ar alewar Dinya da Madi, inda aka koyar da mazauna ‘kauyen Rajun Dinya na karamar hukumar Dutse fasahar zamani ta sarrafa ganyen bishiyar dinya da ‘ya ‘yanta.
Jiya jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta fitar da jadawalin zaben fitar da ‘yan takara a matakai daban daban tare da bayyana kudaden da kowane dan takara zai kashe ya sayi fom din shiga zabe.
Gwamnatin tarayya za ta dauki matakan gyara a shirinta na ciyar da daliban Firamare a fadin kasar.
Kimanin wata guda bayan mataimakin gwamnan Kano farfesa Hafizu Abubakar ya yi murabus, har yanzu gwamna Abdullahi Umar Ganduje bai kai ga nada sabon mataimaki ba.
Yau take ranar bukukuwan bada agaji da ayyukan jin ‘kai a fadin duniya.
Manoma Tumatir a Najeriya sun ce hukumar kwastam da takwararta ta NAFDAC mai kula da harkokin ingancin abinci da magunguna ta kasa, sun sa sun yi asarar kimanin Naira Miliyan dubu goma a kakar noman tumatir ta bana.
A Najeriya masu fashin bakin al’amurran yau da kullum sun suna ci gaba da bada fassarar da bamdabam dangane da batun toshe kofar shiga majalisar dattawa da jami’an tsaro su kayi, wanda ya janyo korar babban darektan hukumar tsaron farin kaya na kasar Lawal Daura.
Manoman shinkafa a jihohin Kano da Jigawa da Katsina sun koka game da tsarin bada lamanin kayan noma karkashin shirin gwamnatin tarayya na tallafawa manoma karkashin kulawar babban bankin Najeriya.
Kimanin shekara guda da zabar Alhaji Abdullahi Yusuf Ata a matsayin shugaban majalisar dokoki ta jihar Kano biyo bayan murabus din tsohon shugaban Kabiru Alhassan Rurum, yau ‘yan majalisar suka kada kuri’ar tsige shi bisa tuhumar rashin iya shugabanci da almundahanar kudade
Cikin makon nan ne kamfanin sadarwa na Google ya kaddamar cibiyar shirin ba da data kyauta a Najeriya, karkashin wani tsari da ake yiwa lakabi da 200 Wi-Fi hotspots.
Manoman shinkafa a jihohin Kano, Jigawa da Katsina sun koka game da tsarin bada lamunin kayan noma karkashin shirin gwamnatin tarayya na tallafawa masu noman karkashin kulawar babban bankin kasar.
Yayin da ya rage ‘kasa da watanni bakwai a gudanar da babban zabe a Najeriya, hada hadar harkokin siyasa sun fara kankama, ta hanyar gudanar da tarukan magoya baya da kuma neman kuri’ar zaben cikin gida na fitar da gwani.
Kungiyoyin fafutikar ‘yanci bil’adama a Najeriya sunce jinkirin tafiyar shari’u a kotuna na daga cikin kalubalen da suke fuskanta wajen gudanar da ayyukan su.
Babbar kotun jihar Kano ta ce umarni da ta bai wa maitaimakin sufeton ‘yan sandan Najeriya mai kula da shiyya ta daya na kamo tare da mika mata shugaban hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano, Muhuyi Magaji ta nan daram.
Majalisar dokkin Najeriya ta amince jiya Laraba da wani kudiri da ke neman Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da anniyar aiwatar da dokar nan mai lamba shida ta kwace kadarorin wadanda ake tuhuma da halatta kudin haram zuwa lokacin da za a kammala shari’un a kotu.
Kungiyoyin neman tabbatar da shugabanci na gari da masu sharhi kan al’amuran yau da kullum na ci gaba da fashin baki dangane da matakan gwamnatoci a najeriya na rarraba kudade ga talakawa a matsayin yunkurin rage radadin talauci a tsakanin al’umar kasar.
Domin Kari