'Yan Najeriya sun fara mayar da martani dangane da furucin gwamnatin kasar cewa, za ta fara raba Naira dubu biyar-biyar ga wasu ‘yan kasar da ke fama da talauci daga cikin kudade fiye da dala miliyan dari uku da ta ce ta karba a hannu hukumomin kasar Switzerland wadanda akace tsohon shugaban kasar Marigayi Sani Abacha ya boye a can.
Babbar kotun Jihar Jigawa ta wanke tsohon gwamnan jihar, Alhaji Sule Lamido daga zargin da gwamnatin jihar ke yi masa na yunkurin tada-zaune-tsaye ta hanyar tunzura magoya bayansa gabannin zaben kananan hukumomin da aka yi a jihar da kuma bata sunan gwamnatin.
Jam’iyyar Young Progressive Party YPP, mai rajin raya siyasar matasa a kasar ta yi taron zauren shawarwari daga al’umma a Kano
Bayan kammala ibadar azumin watan Ramadan miliyoyin mutane sun halarci sallar idi a ko ina a fadin Najeriya.
Yau shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Sarki na Morocco Muhammad na 6 suka rattaba hannu akan wata yarjejeniya kan wasu muhimman batutuwa da suka shafi ayyukan noma da tattalin arziki. Daga Kano Mahmud Ibrahim Kwari ya hada mana rahoto dangane da kunshin yarjejeniyar
Gwamnatin Tarayyar Najeriya tace shirin ciyar da kananan yara da abinci a makarantu ya samar da ayyukan yi ga mata dubu tamanin da bakwai, yayinda kananan yara miliyan biyu da dubu dari biyar suka amfana da shirin a jihohi ishirin da hudu na kasar
Matasa a Najeriya sun fara bayyana farin ciki dangane da alkawarin shugaba Muhammadu Buhari na sanya hannu akan dokar rage shekarun tsayawa takarar zabe a kasar domin baiwa matasan damar shiga a dama dasu a fagen siyasar kasar.
Farfesa Yemi Osinbajo ya kai ziyarar aiki birnin Kano, inda ya tabbatar da shirin gwamnatin tarayya na tallafawa 'yan kasuwa da kananan masana'antu.
Hukumar EFCC ta gurfanar da Jagororin Jam’iyyar PDP a jihar Kano da kuma tsoffin ministocin tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan a gaban babbar kotun tarayya da ke Kano a yau Alhamis, bisa laifin halatta kudin haram a yakin neman zaben Jam’iyyar na 2015.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa jihar Jiagwa domin ziyarar aiki ta yini biyu, inda zai bude tare da kaddamar da wasu aikace-aikace da gwamnatin jihar ta aiwatar.
An shiga makon da ake rigakafin cututtuka masu saurin hallaka kananan yara a sassan duniya, wadda aka saba gudanarwa a karshen watan Afrilun kowacce shekara.
Mallam Aminu Kano da ya kasance daga cikin fitattun 'yan siyasa daga arewacin Najeriya musamman wajen kafuwar Jam'iyyar NEPU mai ikararin kwatarwa talakawa 'yanci ya cika shekaru 35 da rasuwa a ranar 17 ga watan Afrilu.
Yayin da ya rage kasa da shekara guda a gudanar da babban zabe a Najeriya, masana kimiyyar siyasa da harkokin dimokaradiyya da ‘yan siyasa a kasar na ci gaba da bayyana ra’ayi dangane da yawaitar amfani da kudi da ‘yan siyasar Najeriyar kan yi, musamman a yayin zabuka.
Ma’akatar lafiya ta jihar Kastina ta tabbatar da cewa mutane fiye da 300 ne suka kamu da cutar sankarau, kuma 30 sun mutu sanadiyyar cutar.
Hukumomin lafiya a jihar Jigawa da ke arewa maso yamamcin Najeriya, sun ce sama da mutane 50 ne suka kamu da cutar sankarau da kuma wasu cutuka na daban a jihar, kuma yanzu haka an tabbatar da mutuwar 14 daga cikinsu.
Jami’ar Sule Lamido da ke garin Kafin Hausa a jihar Jigawa za ta samar da gurabe ga dalibai daga kasar Gambia, domin yin karatu a wasu darrusa.
Kungiyar cibiyar waiwayen al'adu da tarihin Hausawa ta shirya taronta na shekara shekara da zummar fadakar da Hausawa akan al'adunsu da harshensu domin kada su sake komawa cikin duhun jahici.
Karkashin sabuwar dokar da jihar ke son kafawa, kowane yankin da ake ajiye akwatin zabe a jihar zai rika samun abinda bai gaza naira dubu 50 a wata ba, domin gudanar da kananan ayyuka na gyara ko raya kasa
A yayin da 'yan rajin dimokuradiyya da ma wasu mutanen Jihar Kano ke yin tur da zaben da aka ce an gudanar na shugabanni da kansilolin majalisun kananan hukumomin jihar a karshen makon nan.