Ganin yadda hare-haren 'yan-bindiga ya yawaita a makarantu a shekarar bara, ya sa wata kungiya mai zaman kan ta shirya taron bita ga Malamai da dalibai don kare kawunan su daka hare-haren.
Gwamnatin jihar Kaduna ta ce an kashe mutane 1,129) a fadin jihar Kaduna a bara, sannan an kiyasta cewa kullum akan sace mutane tara a fadin jihar.
Wasu al'umomin garuruwa 11 dake karamar hukumar Birnin Gwari, a jihar Kaduna, sun ce sun hada sama da naira miliyan 30 a matsayin kudin neman sasantawa da 'yan bindiga.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce ayyukan cigaban da gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasuru Ahmed El-rufa'i ya yi sun sa ya kasa kai kanshi gida duk da shekarun da ya yi a matsayin mazaunin Kaduna kafin zama shugaban Kasa.
Sai dai hukumomin tsaro na ikirarin cewa suna samun nasara akan 'yan fashin dajin a hare-haren da suke kai musu.
Sai dai tare hanyar da suka yi a ranar Laraba ya yi wa 'yan-bindigan tutsu saboda da yawan matafiyan sun kubuta.
Watanni shida bayan sace daliban makarantar Bethel Baptist dake Kaduna, har yanzu akwai ragowar dalibi guda da 'yan-bindiga ba su sako shi ba.
A karo na uku a jere cikin wannan mako 'yan-bindiga sun sake tare hanyar Kaduna-zuwa Birnin Gwari inda su ka datse ayarin motoci masu rakiyar jami'an tsaro, su ka kashe mutane sannan su ka sace wasu da dama.
Al'umomin garuruwan da 'yan-bindiga su ka kai hari a karamar hukumar Giwa sun ce bayan mutane 38 da aka yi jana'izar su jiya Lahadi har yanzu ana cigaba da neman wasu mutane da ake zaton su ma an kashe su,
Sanar da sabon tsarin aikin kwanaki hudu a mako da gwamnatin jahar Kaduna ta yi ya jawo cecekuce har ma kungiyar Kiristoci ta Kasa CAN, reshen jahar Kaduna na cewa akwai lauje cikin nadi game da sabon tsarin aikin.
A karshe dai gwamnatin jahar Kaduna ta sanar da bude hanyoyin sadarwar da ta rufe na kusan watanni biyu sai dai ta ce sauran dokokin da aka sa su na nan ba a janye su ba.
Wasu Masana harkokin tsaro sun jingina adadi mafi rinjaye da aka samu na hare-haren 'yan bindiga a jihar Kaduna da irin matsayin da gwamnatin jihar ke kai na cewa babu sulhu tsakanin gwamnati da 'yan bindiga.
Sa'o'i kadan da sace ma'aikatan karamar hukumar Zaria da 'yan-bindiga su ka yi, gamayyar kungiyoyin Arewa ta ba da kashedin karshe game da hauhawar hare-haren 'yan-bindiga a yankin.
Ganin yadda 'yan-bindiga ke cigaba da afkawa garuruwa da kuma sace mutane don neman kudin fansa duk da matakan da gwamnonin Arewa maso yamman su ka dauka ya sa wasu kiran sauya salo.
Sanata Shehu Sani ya yi bayanin yadda jirgin kasan da su ka shiga zuwa Abuja ya sha da kyar bayan harin 'yan-bindigan da ya ce ya lalata hanyar dogon a tsakanin Rijana da Dutse. Saurari rahoton Isah Lawal Ikara
A karon farko tun bayan sanar da rufe hanyoyin sadarwa da kuma hana hawa babura a Kaduna, wasu 'yan-bindiga sun sace wasu dalibai uku a makarantar St. Albert dake karamar hukumar Jama'a ta jahar Kaduna.
A cikin shirin na wannan mako an yi nazari ne akan maganar amfani da na'urorin zamani wajen zabubbuka da kuma tattara sakamako sai kuma maganar maida mulkin kasa kudanchin Najeriya da kuma takaddamar gidan Talabijin na Channels da kuma hukumar kuda da kafafen yada labaru ta Najeriya NBC.
Mako daya da kulle kasuwanni biyu a jihar Kaduna, gwamnatin ta sake sanar da kulle dukkanin kasuwannin mako dake kananan hukumomi biyar da ke shiya ta biyun jihar har sai abin da hali ya yi.
Domin Kari