“Gwamnatin jihar Kaduna ta ba da umarnin rufe kasuwannin na sati-sati na garin Ifira da kuma garin Sabon Birnin Daji.” In ji Samuel Aruwan.
Kungiyar al'umar kudancin Kaduna wato SUKAPO ta tabbatar da sace Sarkin masarautar Jaba Kpop Ham na Jaba, Mr. Janathan Danladi Gyet Maude a ranarLitinin.
Jawabin janyo hankalin duniya da Shugaban darikar Katolika na Sokoto, Rev. Matthew Hassan Kukah ya yi game da yadda matsalar tsaro ke afkawa Kiristoci a Najeriya, na ci gaba da janyo hankalin kungiyoyi da kuma masana tsaro a Najeriya.
A daidai lokacin da ake ta yada cewa 'yan-bindiga sun bukaci miliyan dari biyu kafin sakin mai-martaba sarkin Kajuru, Alh Alhasan Adamu, sarkin ya dawo gida da yammacin yau litinin ba tare da wata rakiyar jami'an tsaro ba.
A yayin da Gwamna Mohammed Bello Matawalle na Jihar Zamfara ke shirin sauya sheka daga Jamiyyarsa ta PDP zuwa APC a ranar Talata, tsohon gwamnan jihar Alhaji Abdul'aziz Yari ya ce gwamnan bai bi ka'idojin da ake bi ba wajen shiga Jamiyyar.
Da alamu dai tsugune ba ta kare ba tsakanin gwamnatin jihar Kaduna dake arewacin Najeriya da kuma kungiyar kwadago game da maganar rage ma'aikatan da ya janyo zanga-zanga da yajin aiki a jihar baki daya.
Hauhawar hare-haren 'yan-bindiga da kuma sace mutane domin neman kudin fansa a Lardin Zazzau ya sa al'umma da malamai da kuma shugabannin yankin shirya taron addu'oin neman mafita game da wadannan irin matsaloli.
Bayan lafawar hare-haren 'yan-bindiga a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, yanzu 'yan-bindigar sun fara tare hanyar Kaduna zuwa Zariya inda a makon nan su ka kashe wasu matafiya sannan suka sace wasu.
Duk da barazanar kama mambobinta a jihar Kaduna, kungiyar kwadago ta kasa NLC, ta fara zanga-zangar gargadi ga gwamnatin jihar game da korar ma’aikatan da ta yi.
Kwanaki kadan bayan sako daliban kwalejin gandun daji da ke Afakan jahar Kaduna, wadanda su ka shiga tsakani don sakin daliban sun ce akwai yiwuwar sakin daliban Jami'ar Greenfield da ke Kaduna.
Duk da barazanar kama mambobin kungiyar kwadagon da su ka shirya zanga-zanga da yajin aikin gargadi na mako guda, Kungiyar kwadagon ta ce daga daren jiya Lahadi za ta dakatar da komai a Kaduna baki daya.
An gudanar da addu'oin neman dauki daga Allah kenan kafin bude bakin Azumin karshe na wannan shekara a masallachin Juma'a na NNPC da ke Kaduna.
A yammacin jiya Laraba ne dai aka sako daliban na kolejin horar da shi'anin gandun daji da ke Afaka a jahar Kaduna i
Al'umomin dake zaune a garuruwan da ke tsakanin Chukun, Udawa, Kuriga da Birnin Gwari sun ce hare-haren'yan-bindiga a yankin ya yi sanadin rashin garuruwan da ba su san adadin su ba.
Kwana guda da sake sace dalibai a jahar Kaduna, gwamnatin jahar ta ce har yanzu ba wani labari game da adadin daliban da aka sace ko kuma inda aka boye su.
A yayin da ake ganin hare-haren 'yan-bindiga sun yi sauki a watan Ramadan, al'umar garuruwan Kuriga da Udawa da kewaye dake karamar hukumar Chukun jahar Kaduna sun ce su hare-haren ma ta'azzara su ka yi a wannan wata na Azumi.
Jami'an tsaro sun yi nasarar ceto 180 daga cikin daliban Kwalejin Gandun Daji da ke Mando, Kaduna wadanda 'yan bindiga su ka yi awon gaba da su, amma saura 30 ba a san inda su ke da kuma halin da su ke ciki ba
Domin Kari