Kwankwaso wanda da mamba ne a jam'iyyar PDP da APC, ya ce ya san raunin dukkan ‘yan takarar kuma ba ya shakkar gamuwa da su ranar zabe.
An ware ranar ce don karfafa muhimmanci kula da tsaftar jiki a lokacin da mace ke al’ada da kuma wayar da kan jama’a.
Gamayyar ‘yan uwan wadanda aka sace iyalan su a jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga watan Maris na shekarar 2022 ne suka gudanar da taron manema labarai, don nuna damuwar su da kuma kira ga gwamnati da dukkan masu ruwa da tsaki da su yi abin da ya dace wajen kubutar da iyalan nasu.
An samu wani mutum dan kasar Birtaniya da ya je Najeriya a ranar 20 ga watan Afrilun shekarar 2022 dauke da cutar ta Kyandar Biri.
Shirin ya zanta ne da Daraktan tsare-tsare, bincike da kididdiga na hukumar lafiya matakin farko ta kasa Dr. Abdullahi Bulama Garba.
Shirin ya fayyace irin nau’ukan ciwon hakori, da alomomin kamuwa da wannan larura da kuma matakan da ya kamata a rika dauka don kare kamuwa da ciwon sai kuma yadda za a dauki matakin yin magani idan mutum ya riga ya kamu da ciwon na hakori.
Yau aka kammala makon da Hukumar Lafiya ta Duniya ta ware don mayar da hankali kan batun yin rigakafi yayin da duniya ke fama da wasu cututtuka masu saurin yado
An ware satin ne don karfafawa mutane gwiwa game da allurar rigakafi don kariya daga cutuka musamman masu yaduwa.
Shirin Lafiya Uwar Jiki na wannan makon ya yi duba ne kan nau'ukan abinci da suka fi dacewa da jikiin dan adam musamman a wannan lokaci na azumin watan Ramadana.
Shirin ya tattauna kan yadda ake kamuwa da cutar ido ta Apolo da kuma matakan da za a dauka wajen magance matsalar.
Shirin ya duba matakan da mai fama da wannan cutar zai dauka da kuma alamominta.
Mata a Najeriya sun dade suna neman a dama da su musamman a fannin siyasar kasar.
A lokacin da ake gab da fara azumin watan Ramadan, ‘yan kasuwa da magidanta na fatan ganin farashin kaya ya sauka don samun sauki ga masu saye da sayarwa.
Cutar basir na daya daga cikin cututtuka da ke addabar jama'a musamman a nahiyar Afirka inda bincine ya nuna cewa, mata ma masu dauke da juna biyu kan yi fama da wannan larura gabanin su haihu.
Shugaban hukumar ta NACA Gambo Aliyu ne ya bayyana hakan a lokacin gabatar da ayukan yaki da cutar a Najeriya daga shekarar 2007 zuwa 2022.
Kungiyar da ke tuna tarihi lokacin da a ka hade kudanci da arewacin Najeriya a 1914, ta ce wasu maso son zuciya da kuma musamman masu fakewa da bambance-bambance don cimma muradun siyasa.
Miyagun kwayoyin wadanda nauyinsu ya kai Kilograms 7.7, an nade su ne a cikin fakiti guda takwas, inda ya sanya su a wurare mabanbanta a cikin kayayyakin da zai yi tafiya da su.
Domin Kari