Gwamnatin Najeriya ta ce tana duba yiwuwar daukar matakan hukunta ‘yan kasar da suka ki amincewa su karbi allurar rigakafin cutar korona.
Kotun masana’antu ta Najeriya ta dage sauraron karar dake tsakanin gwamnatin kasar da likitoci zuwa ranar 16 ga watan Satumba 2021.
A ragar Alhamis ne Najeriya ta karbi allura riga-kafin cutar korona nau’in J&J kimanin dubu 176,000.
Asusun tallafawa kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF ya ce fiye da kashi 50 na yaran da ake haifa a Najeriya ba su da rigista.
Tun da farko dai an shirya fara gudanar da allurar rigakafin ne a yau Talata 10 ga watan Agusta sai aka dage domin baiwa hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC da sauran hukumomin lafiya damar gudanar da bincike domin tabbatar da ingancin allurar.
Hukumar kula da lafiya matakin farko ta Najeriya PHCDA tace za’a fara aikin gudanar da rigakafin annobar cutar korona nau’in moderna da gwamnatin Amurka ta baiwa Najeriya.
Kungiyar likitocin Najeriya ta fara yajin aiki na sai baba ya gani a jiya litinin 2 ga watan Ogustan 2021 sakomakon rashin ciki alkawarin yarjejeniyar da ta kulla da gwamnatin kasar
Barde yace akan ware naira miliyan 49 ga makarantun sakandare 42 a jihar, da ke da yawan dalibai 16,411 a kasafin kudin jihar a duk shekara, inda ya bayyana hakan a matsayin wata kulalliya ta yin almundahana.
An kafa kwamitin bincike akan mataimakin shugaba da jami'an hukumar gyara hali ta Najeriya a jihar Filato, sakamakon tserewa da wasu fursunoni suka yi daga babban gidan yari da ke jihar.