A lokacin da muke gab da shiga sabuwar shekara, shirin lafiya uwar jiki zai yi bitar wasu muhimman maudu'ai da muka tattauna akai.
An gudanar da taron rantsar da sabbin shugabannin kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah da aka zaba bayan kammala wa’adi na tsoffin shugabannin kungiyar na wa’adi biyu a tsawon shekara 8 karkashin Muhammad Kiruwa Ardon Zuru.
Sashen tattalin arziki da zamantakewa na Majalisar Dinkin duniya ya fitar da wani rahoto dake nuna cewa yawan mutane a Najeriya ya kai miliyan 216 a shekarar 2022, da hakan ya kai kashi 2.7 na al’ummar duniya.
Hukumar alhazan Najeriya NAHCON ta bayyana cewa za ta fara tattaunawa da hukumar aikin hajji da umrah ta Saudiyya don fara yarjejeniyar aikin hajjin badi.
An gunadar da bukin yaki da ciwon suga da kuma ake kira ciwon sukari na Hukumar lafiya ta duniya bana da taken 'Samun ilimi game da ciwon sukari don kariya. '
Hukumar lafiya ta duniya ta ware ranar 24 ga watan Oktoba na kowacce shekara a matsayin ranar yaki don kawar da cutar shan inna a duniya.
Kungiyar masu gwanjon kayayyaki ta Najeriya tayi zargin cewa hukumar hana fasa kwauri wato kwastam na saka son zuciya da almundahana game da yadda take gudanar da ayyukan ta.
A duk shekara likitoci a bangaren maganin cutar daji kan hallara don tattaunawa da fadakarwa kan sabbin hanyoyin maganin cutar ta daji.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da kwamiti na musamman mai mutum 16 don kawo karshen zazzabin cizon sauro a kasar karkashin jagorancin attajiri Alhaji Aliko Dangote.
Farashin raguna kan kama ne daga N160,000 zuwa N170,000, wadanda kuma ake shigo da su daga sauran kasashe makwabta Najeriya kuma, sukan kai kimanin N600,000 zuwa N700,000.
Wakiliyar Muryar Amurka Hauwa Umar ta kai ziyara kasuwar Apo da ta Wuse a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya inda ta tattauna da wasu 'yan kasuwa.
Shirin ya samu zantawa da kwararriyar likitar fata, Dr. Zainab Babba Kaita, wacce ke aiki a asibitin gwamnatin tarayya na Abuja
Jam’iyyar hamayya ta NNPP a Najeriya, ta ce ta na daukar matakan kawo karshen mamayar dandalin siyasa da jam’iyya daya ko biyu ke yi kan madafun iko.
Shirin ya karbi bakuncin kwararren likitan kwakwalwa, Dr. Sa'adu Habu na babban asibitin Maradi, inda ya bayyana mana illar shaye-shaye miyagun kwayoyi ga lafiyar jiki da kuma kwakwalwar dan adam.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce jam’iyyar su na maraba da wadanda za su so hada kai da su don babban zaben 2023
Matsalar rashin haihuwa a tsakanin ma’aurata ta zama ruwan dare a sassan duniya, sai dai kwararru na cewa akwai hanyoyin da ake bi wajen kokarin gano inda matsalar take.
Domin Kari