Kasa da kwanaki 11 da za’a gudanar da zaben shugaban kasa da ‘yan majalisun tarayya a Najeriya, jam’iyyu daban-daban na ci gaba da bayyana hanyoyin da za su tafi da harkoki a kasar idan suka sami nasara.
Wasu masu ruwa da tsaki na gargadi kan rudamin da ka iya biyo bayan watsi da umurnin tsawaita lokacin cikar wa'adin daina amfani da tsoffin takardun naira.
Tsohon babban hafsan hafsoshin Najeriya, Janar Tukur Buratai, mai ritaya ya bukaci al’ummar kasar su kwantar da hankulan su yana mai bayyana cewa a bisa dukkan matakan tsaron da hukumomin tsaron kasar suka dauka ya zuwa yanzu, za’a gudanar da zaben ranar 25 ga Fabrairu cikin zaman lafiya da lumana.
Wata cibiyar binciken kwayoyin halittar dan Adam ta kasa, ta ce cututtukan da aka yi watsi da su, na haifar da tarin matsalolin rashin lafiya, masamman ga masu karamin karfi a duniya.
A ranar Litinin jihohin Kaduna, Kogi da Zamfara suka shigar da kara a kotun inda suka kalubalanci sabon wa’adin, wanda zai kare a ranar Juma’a mai zuwa.
Masana na ganin zogale da Malambe a matsayin kayan abinci masu gina jiki dake amfani musamman ga lafiya. Abubuwa masu gina jiki dake cikin nau’ukan abincin sun zarce na sauran nau’ukan abinci, lamarin dake bada gudummawa ga lafiya a cewar masana abinci.
A yayin da ake daf da gudanar da manyan zabuka na shugaban kasa, ‘yan majalisun tarayya, gwamnoni, da na ‘yan majalisun dokokin jihohin kasar 36, akwai muhimman bayanai dabam-daban a kan jihohin Najeriya da irin abubuwan da suka bambanta su da juna.
A cewar kungiyar dakile cutar kansa ta kasa da kasa, yankin kudu da hamadar sahara ne ke da mafi yawan masu fama da cutar kansar mahaifa a duniya.
Karin kwana goman na zuwa ne yayin da ya rage kwana biyu wa'adin da aka diba na daina karbar tsofaffin kudaden ya cika.
Masana na ci gaba da wayar da kan 'yan Najeriya game da manufofin manyan ‘yan takarar shugabancin kasar, inda suka mayar da hankali kan tabbatar da cewa duk wanda ya yi nasara ya cika alkawuran da ya dauka.
Biyo bayan kwashe sama da watanni 30 da ci gaba da zirga-zirgar neman kotu ta kwato musu filayensu na kasuwanci da aka kwace ba bisa kai’da ba, wata babbar kotun tarayya dake zamanta a yankin Kuje na birnin Abuja, ta zartar da hukuncin kwato masu hakkinsu.
Yayin da ake cigaba da kiraye kiraye ga hukumomi da su kara wa'adin daina amfani da tsoffin kudaden Naira, ita kuwa hukumar Babban Bankin Najeriya (CBN), ta ce babu gudu ba ja da baya game da wa'adin
A yayin da ‘yan takara karkashin inuwar jam’iyyu daban-daban ke ci gaba da yin gangamin yakin neman zabe a fadin Najeriya don Talata kan su ga masu kada kuri’a a babban zaben watan febrairu.
Duk da cewa tsayawa a yadda zuciya ke aiki kwatsam ya sha bamban da ciwon zuciya, masana sun ce tsayawar a yanayin da zuciya ke aiki ba zato ba tsammani kan faru a lokacin da zuciya ta sami wani tsaiko kuma ta daina bugawa.
Masu haya a manyan biranen Najeriya kamar Abuja, Legas, da Fatakwal, na kokawa a kan yawan karin kudin haya daga kaso 50 zuwa sama da masu gidajen haya ke yi ba tare da la’akari da halin da ake ciki na matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa a kasar ba.
A wani mataki na farfado da kuma inganta bangaren ilimi a Jihar Zamfara, gwamna Bello Matawalle ya amince da shawarwarin masu ruwa da tsaki na bangaren ilimi na daukan sabbin malamai 412.
Masana a fannin kiwon lafiya sun bayyana cewa wasu sabbin iyaye mata suna fuskantar damuwa bayan haihuwa ko PPD a turance, wanda ka iya zuwa da sauki ko kuma matsananciyar damuwa bayan sun haihu, lamarin da zai iya ɗaukar tsawon makonni ko watanni.
Iyayen sauran dalibai kwalejin tarayya ta Yawuri da su ka rage a hannun maharan da suka yi garkuwa da su sama da watanni 19 da su ka shige sun bayyana takaicin gazawar gwamnati a kokarin ceto su.
A cewar wani rahoton bincike da aka wallafa a mujallar kimiyya ta sanin halayyar dan Adam da zamantakewa akalla kaso 55 cikin 100 na kudurorin sabuwar shekara suna da alaƙa da lafiya.
A wannan makon, shirin Lafiyarmu zai yi waiwaye a kan abubuwan harkokin lafiyar al’umma da suka faru a shekarar 2022, musamman irin nasarori, nakasu da aka samu. Mun ji ta bakin al’umma a game da irin nasarorin da suka samu a game da kudurorin da sukayi na kula da lafiyarsu a wannan shekara.
Domin Kari