Yayin da a Najeriya ake fuskantar kalubale da suka shafi laifukan fyade da cin zarafin mata da kananan yara da sauran kasha-kashe marasa dalili, masana harkokin shari’a a matakai daban-daban na ganin yadda tsarin shari’ar kasar ya ci karo da al’adu, yanayin zamantakewa da kuma addini.
Bincike ya yi nuni da cewa a akasarin lokaci bayan shagulgula mutane na samun karin yawan sinadarin Cholesterol, cututtukan zuciya, hawan jini da karuwar sukari.
Gwamnatin Najeriya ta bayyana jin dadi matuka ga aikin maido wa kasar kayayyakin al’adu da tarihinta na masarautar Benin dake jihar Edo 20 da kasar Jamus ta yi bayan da turawan mulkin mallaka suka sace su shekaru 120 da suka gabata.
A wannan makon, shirin lafiyarmu zai yi nazari kan yanayi ko sosawar zuciya da masoya wasanni daban-daban ke shiga ko samu da kuma abinda zai haifar musu.
Yadda Cutar Dajin Gaban Namiji Ko Kuma Prostrate Cancer A Turance Ke Shafar Maza A Nahiyar Afrika
Bankin CBN ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su kwantar da hankulansu a game da tsarin saboda an yi ne don ci gaban kasa, ba wai don kuntatawa al’umma ba.
Babban Bankin Najeriya CBN ya bayyana cewa, ya gabatar da sabon tsarin daukar kudi ne da nufin rage tsabar kudin da ke hannun jama'a.
Jakadan Najeriya a kasar Rasha, Farfesa Abdullahi Yibaikwal Shehu, ya ja hankalin sabbin daliban Najeriya da suka iso kasar Rasha a bisa tsarin tallafin karatu tsakanin Najeriya da kasar Rasha na shekarar 2022 zuwa 2023.
A wannan makon, shirin Lafiyarmu zai maida hankali ne a kan ranar yaki da cuta mai karya garkuwar jiki wato AIDS wacce aka ware 1 ga watan Disamba don wayar da kan al’umma a kan cutar Musamman yadda kwararru suka ce ana ci gaba da samun rashin daidaito a yaki da cutar.
A daidai lokacin da ake ganin kamata ya yi Najeriya ta kara himma wajen aikin cimma kudurorin nan 17 na raya kasashe wato SDGs na MDD don kawo karshen talauci baya ga tabbatar da wadata ga kowa da kowa, Najeriyar da ma MDD sun rattaba hannu a kan tsarin hadin gwiwa na shekarar 2023 zuwa 2027.
“Yanzu mun saka na’urar da za mu iya ganin jirgin nan daga tashinsa har isar shi. Akwai na’urori da za sui ya gaya mana ko akwai matsala.”
Sama da watanni 7 da dakatar da zirga zirga tsakanin Abuja da Kaduna, sakamakon harin 'yan ta’adda, Ma’aikatar sufuri da hukumar NRC sun gudanar da jigila ta gwaji daga Abuja zuwa Kaduna don da duba matakan tsaro da gwamnati ta dauka a kan hanyar dai sauransu.
A wannan makon, shirin Lafiyarmu zai maida hankali ne kan raunukan da ake samu a wasanni da kuma yadda za’a iya kare Kai daga samun raunukan yayin da aka fara gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya a kasar Qatar.
Babban kwamandan rundunar tsaron sibil defence, Farfesa Ahmad Abubakar Audi, ya ce mata sun fi mayarda hankali a kan aiki idan aka basu dama shi yasa hukumar NSCDC ta kafa punduna ta musamman don taimakawa matan da su suka fi tagayyara idan aka fuskanci wani tashin hankali.
Tsarin narkewar abinci a ciki ya haɗa da sashin hanji ko gastrointestinal ko abunda ake kira GI, cikin mutum, ƙanana da manyan hanji, da gabobi kamar su hanta, dake taka muhimmiyar rawa wajen mai da abincin da muke ci ya zama mai amfani ga jiki.
Hakan na faruwa ne yayin da shi ma Kanu ya ki yarda ya bayyana a gaban kotu saboda yana kulabalantar kin bin umarnin kotun daukaka kara da hukumomi suka yi
Duk da cewa Naira ta fara farfadowa daga faduwa da ta yi a cikin makonnin 2 da suka gabata har ta kai ga naira 910 a bisa dala 1 wanda yanzu an sami farfadowa da kaso 20.8, naira ta koma 720 a bisa kowacce dala 1, masana tattalin arziki na ganin salon da aka dauka ke karya lagon darajar Naira din.
Masana na hasashen cewa sauyin yanayi zai ƙara yin barazana ga lafiyar ɗan adam, musamman a cikin al’umomi masu karamin karfi.
Wata babbar kotun birnin tarayya ta yankewa Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar EFCC hukuncin zama a gidan kaso sabili da gazawar hukumarsa na kin bin umarnin kotu na baya.
A Najeriya, masana sun kiyasta cewa mata dubu 17 ne ke mutuwa a duk shekara sakamakon kamuwa da cutar sankara ko kansar mama saboda yadda akasarin masu fama da cutar ba sa zuwa asibiti a kan lokaci.
Domin Kari