Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari na daga cikin mutanen farko da suka kada kuri’unsu a garinsa na haihuwa Daura, lokacin da aka bude runfunan zabe a yau Asabar.
A cikin kasar da 'yan siyasa dattijai maza ne suka mamaye, Zainab ta fito fili. Ita mace ce. Mara aure. Kuma mai shekaru 26. Ga wasu masu jefa kuri'a a Nijeriya, wadannan kadai sun isa su hana ta shiga zabe.
Jami'an Los Angeles sun ce shirin girgizar kasar na buƙatar aiki sosai da dama, ciki har da ƙarfafa mazaunan don shirye-shiryen bala'i da kayan aikin gaggawa.
Alamu na nuna cewa ta yiwu Amurka da China su cimma yarjejeniya don kaucewa karin haraji.
'Yan majalisar wakilan Amurka na yinkurin kalubalantar matakin da shugaba Trump ya ayyana don ginin katanga a kudancin iyakar kasar.
A halin yanzu wasu yankunan Amurka kamar Philadelphia suna fama da yaduwar kwayar opioid, birnin da huskanci mutuwar sama da mutane dubu da dari daya a bara sakamakon shan kawayar fiya da kima.
Ta ce ta kan dauki samfarin dinki a wajen kawayenta, ko a jikin mutune. Da zarar ta ga dinki, lallai zata iya dinkawa kuma tana iya dinka makamanci wanda aka kawo mata.
King A, ya ce ko da ya fara waka, ya fuskanci matsaloli da dama. Ya ce soyayya ce ta sa ya fara waka. Soyayya da wata budurwar da aka hana shi ne ya sa ya fara waka.
Ana sa ran majalisar dokokin Amurka za ta jefa kuri'a yau Alhamis a kan yarjejeniyar samar da kudade don kaucewa matakin sake dakatar da wasu ma’aikatun gwamnati, yayin da ‘yan majalisar ke samar da kudade don gina shingaye da daukar wasu matakan tsaro a bakin iyakar Amurka da Mexico.
Jaridar Washington Post ta fada a ranar Alhamis cewa wannan itace tara mafi yawa da aka taba dorawa akan duk wani kamfanin fasaha. Jaridar, wacce ta ruwaito kalaman wasu da bata ambaci sunayensu ba, ta ce har yanzu bangarorin biyu ba su amince a kan adadin kudin ba.