Ana sa ran majalisar dokokin Amurka za ta jefa kuri'a yau Alhamis a kan yarjejeniyar samar da kudade don kaucewa matakin sake dakatar da wasu ma’aikatun gwamnati, yayin da ‘yan majalisar ke samar da kudade don gina shingaye da daukar wasu matakan tsaro a bakin iyakar Amurka da Mexico.
‘Yan majalisar dokokin da ma'aikatan su sun yi ta aiki har zuwa daren jiya laraba don yanke shawara akan dokar da ta fito daga wani kwamitin na ‘yan Democrat da Republican da aka dorawa nauyin samar da yarjejeniya akan tsaron iyaka.
Wannan kwamitin shine ya nemi hanyar kawo karshen dakatar da wasu ayyukan gwamnati na tsawon kwanaki 35 da aka yi a watan da ya gabata, a lokacin da kawunan 'yan jam'iyyar Republican da Democrats suka rarrabu a kan bukatar Shugaba Donald Trump ta a ba shi kudi dala biliyan 5.7 don gina Katanga a kudancin iyakar kasar.
Facebook Forum