‘Yan Najeriya na ci gaba da nuna rashin jin dadi, yayin da fatansu na samun sa’ida idan matatar mai ta Dangote ta fara sayar da man fetur a kasar, ya ke neman gushewa; Kungiyar likitocin koda a Najeriya ta ce fiye da mutane miliyan 27 ne ke fama da cututtukan koda, da wasu rahotanni
Kungiyar Hezbullah ta harba jerin makaman roka zuwa yankin arewacin Isra’ila a yau Alhamis, inda ta ci gaba da musayar wuta da dakarun Isra’ila a dai dai lokacin da fargabar kazancewar yaki ke karuwa.
A jiya Talata, gwamnatin tarayyar Najeriya ta gargadi al’ummar kasar game da ruwan da za’a saki daga madatsar lagdo dake kasar kamaru.
Babu cikakkun bayanai game da halin da yanayin tsaro ke ciki a kasar Mali a yau Laraba bayan da a jiya Talata wasu masu tada kayar baya suka afkawa kwalejin horas da jami’an ‘yan sanda da wasu muhimman wurare.
A yau Laraba aka ce tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya amsa gayyatar da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta yi masa.
Domin Kari