Matatar man Dangote ta Najeriya ta fara sarrafa man fetur bayan tsaikon da aka samu sakamakon karancin danyen mai a baya-bayan nan, in ji wani jami'in gudanarwa a ranar Litinin kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito.
A ranar Litinin ne Najeriya ta tuhumi wasu mutane 10 da laifin cin amanar kasa da kuma hada baki wajen tunzura sojoji su ta da kayar baya, bayan zanga-zangar da aka yi a fadin kasar a watan da ya gabata, inda dubban mutane suka fantsama kan tituna domin nuna adawa da matsalar tsadar rayuwa.
Daruruwan masu fama da zazzabi suna kwance a kan siraran katifu a kasan wani wurin da aka keɓe masu jinyar cutar mpox a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, yayin da ma'aikatan asibiti ke fama da matsalar ƙarancin magunguna da kuma ƙarancin sararin daukar marasa lafiya.
Ambaliyar ruwa na ci gaba da yin mummunar barna a jamhuriyar Nijar da Najeriya; Wani matashi a Najeriya yana hada wayoyin USB na cajin waya da sarrafa kwamfuta; A Amurka kuma Robert F. Kennedy Jr, ya sanar da goyon bayanshi ga Trump, da wasu rahotanni
Obi ya ce bai kamata irin wadannan maganganu na raba kan jama’a su samu gurbi a cikin al’ummarmu ba, shi ya sa kowa ya yi watsi da shi.
Onwenu ta rasu ne a ranar 30 ga Yulin shekarar 2024, a asibitin Reddington da ke Ikeja a jihar Legas.
Domin Kari