A Lokacin da yake Magana a taron manema labarai bayan tattaunar da suka yi a Tokyo, Trump ya ce shi yadda yake kallon gwaje-gwajen makaman na Korea, dabara da shugaba Kim Jong Un ke nuna ta neman a kula shi.
Yayin da shugaba Donald Trump ke ziyara a Japan, mataimakinsa Mike Pence, ne ya ajiye furanni a gaban kabarin wani soja da ba’a san sunansa ba a makabartar da ke Arlington
A hirar da a ka yi da Barrista Sadiya, ta ce suna ba da wannan tallafi ne domin taimakawa marasa karfi ganin wannan watan lokaci ne na taimakawa.
Daruruwan mutane maza da mata ‘yan asalin yankin Diffa mazaunan birnin Yamai ne suka hallara a taron da kungiyarsu ta kira da nufin tattaunawa kan matakan tsaro domin gudanar da ayyukansu ba tare da wata fargaba ba.
Majalisar wakilan Najeriya ta amince da kudirin hana anfani da jakkar leda wajen saye da sayarwa a wurare daban daban a cikin kasar.
A Jamhuriyar Nijer, cinkoson jama’a a manyan birane wanda ya samo asali daga karuwar yawan al’umar kasar ya haddasa karancin ruwan sha, lamarin da ya sa gwamnatiin kasar ta soma daukar matakai domin magance wannan matsalar.
Fayfan bidiyon wanda hukumomin Nijar suka haramta wallafa shi ta kowace irin kafa na dauke ne da wani sako wanda a cikinsa Hama Amadou ke nuna jin takaici akan abin da ya kira gazawar gwamnatin Nijar wajen shayo kan matsalar tsaro.
Hira da Malam Abba Ibrahim Abubakar a kan muhimmancin daren Lailatul Kadr ga Musulmi.
Shugaban kasar Nijar Issouhou Mahamadou ya tattara manyan hafsoshin soja da jakadun Amurka da Faransa, a yinkurinsa na sake damara don inganta tsaron kasar, mako guda bayan mummunan harin da ya hallaka sojojin Nijar.
A hirar da aka yi da Malam Muktar Umar Sharada ya bayyana falalar goman karshe na watan Ramadana.
Hukumomin Aikin Hajji na jihohi a Najeriya na ci gaba da bayyana cewa kudin kujerar Hajjin bana bai gaza naira miliyan 1.5.
Da shiga goma ta tsakiya na watan Ramadana, lokaci ne da matasa da yara suke yin tashe.
Ofishin jakadancin Amurka a jamhuriyar Nijar ya shirya liyafar bude baki ma Musulmin kasar, a albarkacin watan Ramadan.
Majalisar Wakilan Najeriya ta amince da wata doka da za ta haramta safarar jakuna, ko sayar da su domin abinci ko cutar da su ta wata hanya ta daban.
Shugaban kasar Nijer Issouhou Mahamadou ya jaddada aniyar ci gaba da jajircewa domin murkushe kungiyoyin ta’addancin dake tada zaune tsaye a kasar da makwaftan ta.
Neymar, dan kungiyar kwallon kafa ta PSG ya bayyana sha'awar sa na fatan cewar kungiyarsa ta PSG tayi kokarin ganin ta siyo Phillipe Coutinho.
Domin Kari