Hira da Muryar Amurka, Malam Mustapha Yunusu ya bayyana muhimmancin tsaftace kayan marmari da ganyaye a watan Ramadana.
An gabatar da wasu kudurori don kyautatawa gwamnan mai barin gado a jihar Bauchi.
Rahoto daga Madina dake kasar Saudia Arabia inda zaku ji yadda tsarin ciyar da wadanda suka zo garin Madina ziyara a hanyarsu ta zuwa sauke Umrah na watan Ramadana.
Hira da Mallam Muktari Muhammad a kan muhimmancin ciyarwa a watan Ramadana, musamman ciyar da marayu da miskinai.
A caigaba da fuskantar kalubalen tsaro da ake yi a yankin Sahel na Afirka, sojoji masu tarin yawa sun halaka, bayan da wasu ‘yan bindiga suka bude wuta a Jamhuriyar Nijer.
Matafiya na cigaba da bayyana ra'ayoyinsu kan matakin da ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya dauka na dakatar da sabunta Visa ta hanyar sako, sai an zo a zahiri
Wasu dalibai a jami’ar Wisconsin-Madison sun kirkiri kafar zamani ga wata Mage.
Koci Kloop ya dau sabon alwashi ga kungiyarsa a kakar bana.
Dan wasan Antoine Griezmann ya ce lokaci yayi da zai raba hanya da kungiyar sa bayan shekaru biyar.
Kwamitin binciken kut da kut na MDD, na kiran kasashen duniya da su yanke hurdar dake tsakanin su da hukumomin sojan kasar Myanmar
Kalaman na Trump na baya bayannan, suna zuwa ne, bayan da ya kara yawan haraji akan kayan China na kimanin dalar Amurka billiyan $200 da ake shigowa da su Amurka, kana da kara harajin akan kayan Chinar da suka kai na kimanin dala billiyan $300.
Shugaban Gasar Amurka Donald Trump ya yi jawabi na hadin kai a fadarsa, a lokacin da ya shirya walimar bude-baki ga jami'an diplomasiyyar kasashen da Musulmi suka fi rinjaye.
Daruruwan Mata a karkashin kungiyar Coalition of Women Group ta Najeriya, sun yi tattaki a birnin tarayya Abuja su na bukatar a basu karin mukaman gwamnati.
Musulman duniya baki daya suna murna da zuwan watan Ramadan, mai girma da albarka
A Burtaniya Yarima Harry da matarsa Meghan sun yi alfaharin bayyana sabon jaririnsu ga kafafan yada labarai na duniya a yau Laraba. Ranar Litini aka haifi jaririn
A kasar Sudan kuma, jiya Talata sojojin da ke mulkin kasar sun ce suna so sabon fannin shari’ar kasar ya zama bisa tafarkin musulinci, bayan sun kwaskware daftarin da shugabanin 'yan adawa na fararar hula ya gabatar.
A jamhuriyar Nijer yau aka fara Zaman makoki na kwanaki uku da nufin nuna alhinin rasuwar mutane sama da hamsin, da suka Kone kurmus.
A jahar Bauchi ma’aikata da kuma 'yan fensho su na cikin yanayin rudani da kuma rashin tabbas dangane da batun biyansu albashi da kuma hakkokinsu.
Domin Kari