Dubun-dubatar masu zanga-zanga sun yi arangama da ‘yan sandan kwantar da tarzoma, Alhamis, 3 ga Satumba, suna masu bijirewa kullen cutar coronavirus don gudanar da bikin addini a Nepal.
Masu zanga-zangar sun taru a garin Lalitpur a kewayen keken hawa mai mutum-mutumin gunkin Rato Machindranath.