A Jamhuriyar Nijar, wani ce-ce-ku-ce ya barke a tsakanin bangarorin kasar bayan da ‘yan adawa suka zargi tsohon shugaban kasa Issouhou Mahamadou da siyen wani fili mallakar gwamnati alhali doka ba ta yarda da haka ba. Sai dai makusantansa na kallon abin tamkar rashin sanin abin fada ne.
Kamfanin Dangote na da kashi 60.6 wanda mallakar Aliko Dangote ne, mutumin da ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka. Sai Lafarge da ke da kashi 21.8 yayin da BUA ke da kashi 17.6
Kwana 1 bayan da rundunar mayakan Chadi ta bada sanarwar murkushe dukkan wani kutsen ‘yan tawayen FACT, Shugaban gwamnatin mulkin sojan kasar General Mahamat Idriss Deby, ya kai ziyara a Jamhuriiyar Nijar a ranar Litinin 10 ga watan Mayu inda suka tattauna da shugaban kasa Mohamed Bazoum a fadarsa.
A cikin shirin na wannan makon mazuna birnin Jos a arewacin Najeriya su na ci gaba da fama da matsalar karancin ruwa, lamarin da ke sa wasu masu sana’o’i amfani da ruwa mara tsafta wajen wanke-wanke da sauran al’amura, da wasu rahotanni.
Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rigths Watch ta bukaci gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum ta gudanar da bincike domin tantance abubuwan da suka yi sanadin mutuwar wasu daruruwan fararen hular da aka sanar cewa ‘yan ta’adda ne suka halaka su a arewacin jihohin Tahoua da Tilabery.
Alamu na dada nuna cewa ‘yan Najeriya sun fara kosawa da rashin hukunta wadanda ake kamawa da ayyukan ta'addanci har suna daukar doka a hannunsu.
Shugaban kasar Nijar Bazoum Mohamed, ya gana da sabon kwamandan rundunar Barkhane mai sansani a yankin Sahel inda suka tattauna akan batutuwan da suka shafi yanayin tsaron da ake ciki a kasashen yankin Sahel.
Daruruwan mutane sun tsere daga garin Shadadi a yankin karamar hukumar Mariga dake cikin jihar Nejan Najeriya bayan da 'yan bindiga suka aukawa garin.
Domin Kari