A cikin shirin na wannan makon a birnin Jos dake Najeriya wata kungiya mai zaman kanta ta dukufa wajen wayar da kan mutane don kaucewa furta kalaman kiyayya dake haddasa munanan rikice-rikice a tsakanin al’umma, da wasu sauran rahotanni.
Gwamnatin Najeriya ta ce duk da biliyoyin Naira da ta fitar karkashin tsare-tsarenta na yaki da fatara ta hanyar tallafawa kanana da matsakaitan masana’antu da sana’oi, domin bunkasa tattalin arziki daga tushe, matsalar annobar coronavirus ta haifar da koma baya ga cimma wannan buri.
A Jamhuriyar Nijar hukumomin kiwon lafiya da hadin gwiiwar kungiyoyi masu zaman kansu na ci gaba da karfafa matakai domin riga-kafin cutar yoyon fitsari yayin da a wani bangare aka fara yunkurin kawo karshen kyamar da mata masu fama da wannan cuta ke fuskanta a sahun al’uma.
Dubban masu zanga-zangar nuna takaicin rashin tsaro a jihar Nejan Najeriya, sun kwashe sa'o'i da dama, inda suka rufe babbar hanyar mota da ta tashi daga Kaduna zuwa babban birnin tarayya Abuja.
Duk da matakan da gwamnatin Nijar ta dauka a shekarun baya-bayan nan don ganin kasar ta samu ci gaba a alkaluman kididigar da hukumar UNDP ke fitarwa a kowace shekara kan batun ci gaban rayuwar jama’a, da alama har yanzu tsugune bai kare ba.
A cikin shirin wannan mako Amurka ta fitar da rahoton shekara-shekara akan ‘yancin yin addini – kuma Nijeriya da Iran da Saudiyya da China su na daga cikin kasashen da rahoton ya ce suka fi takurawa jama’a, da wasu rahotanni.
“Jita-jita ce. Muna kan bincike. Ba za mu iya cewa komai ba sai mun tabbatar da aukuwar hakan,” In ji Yerima.
Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta yi karin haske game da abubuwan da suka faru da wasu ‘yan kasar mazauna Cote d’Ivoire sakamakon yamitsin da ya barke ranar Larabar da ta gabata a birnin Abidjan inda aka kwashi ganima a shagunan ‘yan Nijar, aka yi masu duka kafin hukumomin Cote d’Ivoire su dauki mataki.
Kamfanin dillancin labarai na AP, ya ruwaito cewa, Messi bai fita atisaye a ranar Juma’a ba.
"Saudiyya ta kashe kusan dala biliyan hudu a fannonin samar da wutar lantarki, fasahar sadarwa, samar da abinci a nahiyar Afirka."
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke cewa ya kamata hukumar ta NITDA ta warware wasu kalubale da suka shafi ayyukanta.
Majalisar kula da harkokin addinai ta Najeriya NIREC ta kalubalanci Gwamnatin kasar da ta kara kaimi wajen magance matsalar rashin tsaro da ke addabar kasar wadda wani sa’ilin ake dangantawa ko dora laifin ga wata kabila ko addini.
A cikin shirin wannan makon a birnin Jos dake arewacin Najeriya, za ku ga yadda kasuwa ta budewa wasu matasa masu kirkire-kirkire da suke sarrafa itace wajen yin cokula da sauran abubuwan kicin, da wasu rahotanni.
Yadda ‘yan ta'adda ke nuna gadara wajen kai hare-hare ga jama'a, na tilas ta shugabannin al'umma jaddada kira ga hukuma da ta yi da gaske wajen shawo kan wannan matsalar.
Domin Kari