Masu sharhi da fashin baki akan harkokin tattalin arziki na ci gaba da mayar da martni akan rahotan baya-bayan nan da bakin duniya ya fitar dake cewa, kalubalen da tattalin arzikin Najeriya ke fuskanta a yanzu ya rusa nasarorin da aka samu a cikin shekaru goma da suka shude.
Shugaba Joe Biden da shugabanni daga kungiyar dimokiradiyya da aka fi sani da G7 sun bayyana kudurinsu na magance matsalar aikin bauta, barazanar fansa, da rashawa.
Lauyoyi a Kano da masu sharhi kan harkokin yau da kullum, musamman a fagen siyasan Najeriya na ci gaba da yin fashin baki dangane da hukuncin babbar kotun tarayya na daurin shekaru 19 ga tsohon dan majalisar wakilai Faruk Lawal.
Da alamu dai tsugune ba ta kare ba tsakanin gwamnatin jihar Kaduna dake arewacin Najeriya da kuma kungiyar kwadago game da maganar rage ma'aikatan da ya janyo zanga-zanga da yajin aiki a jihar baki daya.
Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari ya mika bukatar karin kasafin kudaden da za a yi amfani da su wajen kawar da barazanar tsaro da ta addabi sassa daban-daban na kasar.
A Jamhuriyar Nijar wasu ‘yan kasar sun fara maida martani bayan kungiyar IS ta dauki alhakin harin da aka kai a gidan kakakin majalisar dokokin kasar Seyni Oumarou dake birnin Yamai a ranar Asabar 12 ga watan Yuni.
Kungiyar kwadago a Jihar Nasarawa da ke tsakiyar arewacin Najeriya ta kasa cimma matsaya da gwamnatin Jihar kan yarjejeniya da zai kawo karshen yajin aiki da ma’aikatan Jihar ke yi.
Sudan ta Kudu, wacce ta sami 'yancinta daga Sudan a shekarar 2011, a mafi yawan kasancewarta, ta fuskanci kalubale iri-iri da suka jefa al’umarta cikin wahala.
Gwamnatin jihar Kano ta rufe ayyukan babban asibitin yara dake kan titin gidan Zoo a Kano shekaru uku bayan asibitin ya fara aiki.
Abubuwa masu ban mamaki da aka samu a cikin shekarun da suka gabata a cikin Ukraine suna cikin haɗari. Muhimman damammaki na saka hannayen jari ds kutsa kai cikin kasuwannin turai na fuskantar barazana
Gwamnatin jihar Nejan Najeriya ta ce zata sanya karfi wajen kubutar da yaran makarantar Islamiyyar Salihu Tanko su 148 dake garin Tegina wadanda ke hannun ‘yan bindiga a halin Yanzu.
A daidai lokacin da gamayyar kungiyoyin arewacin Najeriya wato CNG ke nesanta kai da gwamnonin kudu da ayyukan kungiyar IPOB mai rajin kafa kasar Biafara da neman kasa ta ci gaba da zama tsintsiya madaurinki daya wasan yara ne kawai, wasu na cewa ‘yan Najeriya mara sa aikin yi ke neman a raba kasar.
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA ta gudanar da taron manema labarai don tattauna ayyukan da za ta gudanar game da ranar yaki da shan miyagun kwayoyi da fataucin su.
Shugaba Biden ya ce “wannan hukunci mai dumbin tarihi, na nuni da cewa duk wadanda suka aikata wasu munanan ayyuka, za su fuskanci kuliya. Sannan hukuncin na kara nuni da yadda muka himmatu wajen ganin an kaucewa sake aukuwar irin wannan danyen aiki a ko ina a duniya.
Bincike na nuni da cewar a Jihar Bauchi ana samun karuwar ayyukan cin zarafin mata musamman fyade wanda a kowacce rana ana samun rahotanni akalla biyar a cewar babban magatakardan manyan kotunan Jihar Bauchi Barrister Emmanuel Sublim.
Shugabannin Fulani da sauran masu fada a ji a yankin Yammacin Najeriya sun yi Allah wadai da wa’adin da Sunday Adeyemo Igboho wani mai ikirarin kare yankin Yarbawa da ‘yan sanda ke nema ya bai wa dukkan Fulani makiyaya mazauna jihohin yarbawa wa’adin ficewa daga yankin kafin ranar Litinin.
Bayanai dai sun nuna cewa jami’an tsaron ‘yan bangar sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suka tunkari ‘yan bingar a kokarinsu na kwato wasu shanu.
A cikin shirin wannan makon tun bayan da Faransa ta sanar da shirinta na janye dakarunta a yankin Sahel na Afirka, jama’a a Mali da Chadi da Nijar ke ta tsokaci game da tasirin wannan mataki akan yaki da ‘yan bindiga masu da’awar jihadi, da wasu rahotanni.
A Najeriya jama'a na kyautata zaton cewa rundunar sojin kasar na can na fafatukar ceto daliban makarantar gwamnatin tarayya dake Birnin Yauri wadanda ‘yan bindiga suka sace.
Domin Kari