Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ba da jimawa ba ta fitar da rahoto na 23 kan ’Yancin Addini na Duniya.
Daya daga cikin daliban makarantar Islamiyyar Salihu Tanko a Tegina dake hannun ‘yan bindiga a jihar Nejan Najeriya da Allah ya bata sa'ar tserewa, ta ce ta sha bakar azabar yunwa da bugu da kuma tafiyar kasa a lokacin da take hannun 'yan bindiga.
Alamu na nuna cewa ‘yan Najeriya sun fara tunanin ba mafita ga matsalolin da suka dabaibaice kasar illa dukufa ga addu'a tare da komawa Ubangiji, tamkar dai yadda malamai suka yi ta kira a can baya.
A cikin shirin wannan makon Najeriya ta na daya daga cikin kasashen duniya da aka fi ta’ammali da miyagun kwayoyi abin da ke yin mummunan barna ga rayuwar matasa, da wasu rahotanni.
Yaya duniya za ta kasance ba tare da tsuntsaye ba? Tsuntsaye ba wai kawai suna da kyau ba ne, suna da mahimmanci ga aikin noma kuma suna taimakawa wajen samar da a cikin muhalli.
Cin hanci da rashawa na kashe aminci, yana lalata ci gaba, yana zubar da amincewa da cibiyoyin dimokiraɗiyya yana kuma bude hanyar aikata laifuka tsakanin ƙasashe.
A Najeriya wannan Alhamis ce cikar mako biyu da sace daliban sakandare a jihar Kebbi dake arewacin kasar kuma har yanzu shuru ake ji, duk da kalaman da gwamna Abubakar Bagudu ya yi na gayyar shiga daji.
Ranar daya ga watan Yuli shugaba Mohamed Bazoum na Nijar ke soma ziyarar aiki a jihar Diffa inda gwamnatin kasar ta kaddamar da ayyukan mayar da ‘yan gudun hijirar cikin gida sama da 200,000 zuwa garuruwansu na asali a ci gaba da karfafa matakan farfado da tattalin arzikin jihar.
A ranar Talata Ministan shari’a Malami Abubakar ya bayyana cewa an cafke Kanu wanda yanzu haka yana tsare a ofishin jami’an DSS yana jiran shari’a.
Gabanin ɓarkewar tashin hankali a 2014, Yemen ita ce ƙasa mafi talauci a Yankin tekun yankin kasashen Larabawa. A yau, Majalisar Dinkin Duniya ta ce Yemen "ita ce kasa da ta fi fuskantar matsalar bukatar agaji a duniya."
Harakoki sun fara dawowa sannu a hankali a jihar Diffa a Jamhuriyar Nijar inda jama'ar yankin ta fara komawa kan ayyukan yau da kullum bayan da aka fara shawo kan matsalar tsaron da aka yi fama da ita a shekarun baya.
Gwamnatin jihar Nejan Najeriya ta sanar da korar ma'aikatanta guda 328 daga bakin aiki saboda samunsu da laifuffuka daban-daban da suka karya dokokin aikin gwamnati a jihar.
A yayin da Gwamna Mohammed Bello Matawalle na Jihar Zamfara ke shirin sauya sheka daga Jamiyyarsa ta PDP zuwa APC a ranar Talata, tsohon gwamnan jihar Alhaji Abdul'aziz Yari ya ce gwamnan bai bi ka'idojin da ake bi ba wajen shiga Jamiyyar.
Saboda matsalar cin hanci da rashawa barazana ce kai tsaye ga tsaron kasar Amurka, yakar wannan masifa da ta addabi duniya ita ce babbar manufar tsare-tsaren cikin gida da kasashen waje na gwamnatin Biden-Harris.
A cikin shirin wannan makon za ku ga yadda jami’an tsaro ke amfani da fasahar gane fuskokin mutane wajen kama masu laifuka a nan Amurka, da wasu rahotanni.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken, a ziyarar aikinsa ta farko a Gabas ta Tsakiya, ya yi tafiya zuwa Isra’ila kwanaki kadan bayan yarjejeniyar da ta kawo karshen fada na kwanaki 11 tsakanin Hamas da Isra’ila.
Domin Kari