Kungiyar Jama’atu Nasril Islam a Jihar Filato ta ce ba ta ba kowa ko wata kungiya damar gudanar da wani tattaki ko zanga-zanga a harbar babban masallacin da ke birnin Jos ba.
Batun dorewar zaman lafiya da hadin kan kasa shi ne ya dauki hankalin da dama daga cikin wadanda suka halarci bikin cika shekara 80 da zagayowar ranar haihuwar tsohon shugaban mulkin soja a Najeriya Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya.
Wasu kungiyoyi da dama a arewacin Najeriya sun yi Allah’wadai da mummunan kisan gillar daya auku kan wasu matafiya da suka ratsa ta jihar Filato a ranar Asabar da ta gabata daga jihar Bauchi zuwa jihar Ondo.
A Najeriya shugaban kasa Mohammadu Buhari ya rattaba hannu a sabuwar dokar Man Fetur ta shekara 2021 wacce aka fi sani da PIB.
Babban Shehun darikar Tijjaniyya a Najeriya Dahiru Usman Bauchi ya ce ba su yarda wasu su dau doka a hannu ta hanyar ramuwar gayya bisa kisan gilla ga mabiyansa ba a Jos, wadanda suke komawa jihohinsu bayan ziyarar da su ka kai masa a Bauchi.
A Jihar Borno a Najeriya hukumar kula da filaye ta jihar ta rushe wata majami’a da ke unguwar Moduganari a babban birnin jihar, hakan yayi sandiyyar mutuwar mutum daya, sannan kuma mutane da dama suka jikkata, da wasu rahtotanni.
‘Yan majalisar dokokin jihar Bauchi sun kammala taron bita na yini biyu a jihar Kano kan sharruda da ka’idojin aiki da dokar ‘yancin kasashe kudade ga majalisun dokoki na jihohi a Najeriya wadda majalisar dokokin kasar tayi kusan shekara guda baya.
A daidai lokacin da matsalolin tsaro ke kara ta’azzara, gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara ya yi kira ga sauran takwarorinsa na arewacin Najeriya da ma gwamnatin tarayyar su hada gwiwa wajen samo mafita mai dorewa.
Wannan Talata 10 ga watan Agusta ce ranar daya ga watan Muharram wata na farko a tsarin shekarar Musulunci wanda ya nuna farawar sabuwar shekarar 1443 bayan hijira.
Wasu 'yan bindiga sun hallaka akalla mutum biyu tare da jikkata wasu da dama, da kuma yin garkuwa da shugaban jam'iyyar APC na yankin Arewacin jihar Neja a Najeriya.
A cikin shirin wannan makon yayin da Najeriya ta haramta fitar da gawayi daga kasar, wasu kamfanoni na amfani da kwakwa don yin gawayi a kokarin rage yawan sare itatuwa, da wasu rahotanni.
A ci gaba da rangadin wasu kasashen Afirka da mataimakiyar Sakataren gwamnatin Amurka mai kula da sha’anin siyasa Ambasada Victoria Nuland ke yi, jami'ar ta yada zango a Jamhuriyar Nijar inda suka gana da shugaba Mohamed Bazoum a fadarsa a yammacin a ganar Alhamis.
Wata kungiya mai suna North Central People’s Forum ko kuma Kungiyar Jama’ar Arewa Ta Tsakiya an dade da kafa ta sai dai yanzu ne Shugaban amintattun kungiyar, Laftana JanarJeremiah Timbut Useini ya kaddamar da mambobin kwamitin da zai gudanar da Kungiyar.
Hukumomin kula da gidajen yari a Najeriya sun ce tanade-tanaden sabuwar dokar kula da ayyukan gidajen yari da majalisar dokokin kasar ta zartar kuma shugaban kasa ya rattabawa hannu a shekara ta 2019 za ta taimaka.
Ranar 3 ga watan Agusta Jamhuriyar Nijar ke ta shekara 61 da samun ‘yancin kai daga turawan mulkin mallakar kasar Faransa.
Iyayen yaran nan da aka sacewa 'ya'ya a Kano kuma aka yi safarar su zuwa jihohin Anambra da Enugu da ke yankin kudu maso gabashin Najeriya sun yi maraba da hukuncin da babbar kotun Kano ta yanke na shekara 104 a gidan gyaran hali.
Hukumomi a jihar Kwaran Najeriya na gudanar da bincike akan kisan wata yarinya mai suna Fatima Abdulkadir ‘yar kimanin shekaru 18 ta hanyar kona ta da wuta.
Domin Kari