A yayin rangadin da ya fara a rasar Lahadi a jihar Maradi, shugban kasar Nijar Mohamed Bazoum ya bayyana shirin kara girke jami’an tsaro da karin kayan aiki a ci gaba da neman hanyoyin murkushe ayyukan ‘yan bindiga da suka addabi al’umar yankin dake samun dubban ‘yan gudun hijira daga Najeriya.
Kuma a jihar Kano a Najeriya za ku ga wata matar aure da take ci gaba da samun tagomashi a sana’ar ta, ta dinka kayan yara ‘yan kanti, da wasu rahotanni.
Gwamnatin jihar Nejan Najeriya ta sanar da rufe wasu makarantu guda 31 saboda matsalar rashin tsaro da ta addabi jihar.
Wadansu mutane da suka kai 50, dauke da manyan bindigogi ne, in ji mutanen garin Kwandamo a cikin karamar hukumar mulkin Illela ta Jihar Sokoto, da ke kan iyaka da birni N'Konni a Jamhuriyar Nijar suka kai harin.
A ci gaba da zagayen al’umomin yankunan dake fama da matsalar tsaro Shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum zai ziyarci jihar Maradi a ranakun 1 da 2 ga watan Agusta, wata guda kenan bayan rangadin da ya gudanar a jihar Diffa yankin da dubban ‘yan gudun hijira suka fara komawa garuruwansu na asali.
Kungiyar al'umar kudancin Kaduna wato SUKAPO ta tabbatar da sace Sarkin masarautar Jaba Kpop Ham na Jaba, Mr. Janathan Danladi Gyet Maude a ranarLitinin.
A lokacin babbar sallah, Musulmai a fadin duniya suna yin hadaya, wato yanka dabbobi domin yin sadaka domin neman lada daga wurin Allah. Wasu ma’aikatan Sashin Hausa na Muryar Amurka sun yi takakkiya zuwa Pennsylvania domin gabatar da wannan ibada.
Masu ruwa da tsaki a Najeriya sun bayyana cewa, abubuwa da dama kamar rashin tsarin gwamnati, bayar da jagoranci ga wadanda ba su cancanta a ba aiki ba na kara ta’azara matsalar zaman kashe wando a kasar.
Kiristocin Najeriya masu ziyara sun tashi a karon farko zuwa kasar Jordan don gudanar da ayyukan ibada tun bayan barkewar Annobar COVID-19.
A cikin shirin na wannan makon a Jamhuriyyar Nijar al’ummomin musulmai sun gudanar da shagulgulan sallah kamar a sauran wurare, da wasu rahotanni.
A daidai lokacin da ake bukukuwan Babbar Sallah a Najeriya, farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabi. Kayayyakin wadanda su ne ake amfani da su a kullum wajen sarrafa abinci sun hada da tumatir , attarahu, tattasai da sauran su.
Wasu da ake zargin masu ta da kayar baya sun kai wa wani kauye mai suna Hinbla hari wanda ke karamar hukumar Madagali a jihar Adamawa inda suka kona gidaje sama da shida kuma aka yi asaran rai guda da dukiyoyi.
Jawabin janyo hankalin duniya da Shugaban darikar Katolika na Sokoto, Rev. Matthew Hassan Kukah ya yi game da yadda matsalar tsaro ke afkawa Kiristoci a Najeriya, na ci gaba da janyo hankalin kungiyoyi da kuma masana tsaro a Najeriya.
Majalisar dake sasanta tsakanin addinai a jihar Filato, ta kalubalanci jami’an tsaro da su gaggauta gano wadanda ke shigar-burtu da kakin soja ko na ‘yan sanda suna hallaka mutane.
A cikin shirin wannan makon lokacin babbar sallah dai, musulmai da Allah ya hore wa su na siyan dabbobi domin yankawa a ranar sallar a matsayin layya. Sai dai a bana lamarin sai a hakali ga mutane da dama., da wasu rahotanni.
Amurka ta ayyana Ousmane Illiassou Djibo - wanda aka fi sani da Petit Chapori - a matsayin Cikakken Dan Ta'adda na Duniya.
Bisa ga yadda hare haren ta'addanci ke ci gaba da jefa rayukan ‘yan Najeriya cikin halin tsaka mai wuya, wasu daga cikin ‘yan kasar na ganin da gwamnatin tarayya za ta baiwa gwamnoni ikon bayar da umurni ga jami'an tsaro da watakila a iya samun saukin matsalolin.
Domin Kari