A cikin shirin na wannan makon wasu Amurkawa da suka kasance a Afghanistan lokacin da gwamnatin kasar da Amurka ke marawa baya ta rushe, sun yi karin haske akan irin tashin hankalin da suka gani yayin da suka bar Kabul don komawa Amurka, da wasu rahotanni.
A cikin shirin na wannan mako an yi nazari ne akan maganar amfani da na'urorin zamani wajen zabubbuka da kuma tattara sakamako sai kuma maganar maida mulkin kasa kudanchin Najeriya da kuma takaddamar gidan Talabijin na Channels da kuma hukumar kuda da kafafen yada labaru ta Najeriya NBC.
Babban Hafsan Hafsoshin rundunar sojojin kasa na Najeriya Janar Farouk Yahya ya bada tabbacin cewa ‘yan bindigan nan da suka kai farmaki makarantar horas da hafsoshin sojojin Najeriya wato NDA za a kamo su kuma za su fuskanci hukunci daidai da abin da shuka aikata.
A Najeriya bisa ga yadda hukumomi a jihohin Arewa ke kakaba dokoki domin neman sauki ga matsalar rashin tsaro, wasu ‘yan kasar na ganin a yi farautar ‘yan bindigar a gama da su zai fi kakabawa mutane dokoki.
A hukumance, Amurka ta mikawa Najeriya manyan jiragen yakin nan na zami wato A29 Super Tucano a wani dan kwarya-kwaryan biki da aka yi a sansanin sojojin saman Najeriya dake filin jirgin saman birnin Abuja.
Gwamnatin jihar Nejan Najeriya ita ma ta sanar da rufe manyan kasuwannin dake ci mako-mako kuma ake sayar da dabbobi a cikinsu a duk fadin jihar.
A Najeriya masana na ganin cewa halin kuncin rayuwa da jama'a ke fuskanta na daya daga abubuwan da ke saka su jefa rayukan su cikin hadari ba tare da la'akari da illolin da abin zai haifar ba.
A Najeriya alamu na nuna cewa jama'a sun fara debe tsoron ‘yan ta'adda domin suna bayar da gudunmuwa wajen kamawa ko kisan barayin, wanda kuma bai rasa nasaba da ganin cewa hukuma ta kasa magance matsalolin.
Mako daya da kulle kasuwanni biyu a jihar Kaduna, gwamnatin ta sake sanar da kulle dukkanin kasuwannin mako dake kananan hukumomi biyar da ke shiya ta biyun jihar har sai abin da hali ya yi.
Yayin da rahotannin safarar mutane domin bautar da su ke karuwa akan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar, masu rajin yaki da wannan dabi’a sunce matakin samar da dokoki na bai daya a kasashen Afrika ta Yamma zai taimaka wajen magance matsalar.
A cikin shirin na wannan makon an sha shagali a fadar shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, yayin da shugaban ya aurar da dan shi na miji guda – Yusuf Buhari, da wasu rahotanni
Al’ummar kauyen Yalwan Zangam a karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato na zaman fargaba da tashin hankali bayan da ‘yan bindiga suka shiga kauyen a daren ranar Talata suka hallaka maza da mata da yara kanana.
Gwamnan jihar Neja a Najeriya Alhaji Abubakar Sani Bello ya ziyarci garin Ma’undu da ‘yan bindiga suka dai daita domin ganema idonsa irin ta’asar da ‘yan fashin daji sukayi ma mutanen wannan gari.
A Najeriya, amincewa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi na samar da wuraren kiwo 368 a Jihohi 25, ya dauki hankalin manya manoman kasar, inda wasun su ke ganin an dauko hanyar magance yawan rikicin da ke faruwa tsakanin manoma da makiyaya.
A cikin shirin na wannan makon masana sun ce ficewar Washington daga Afghanistan bayan shekaru 20 zai iya yin tasiri na dindindin kan tsayuwar Amurka a kasashen waje, da wasu rahotanni.
A yanzu dai wadannan yara sama da dari suna cikin makonni 11 kenan a hannun wadannan ‘yan fashin daji ba tare da samun nasarar kubutar da su ba.
A Najeriya masana na ci gaba da tattaunawa akan sahihan hanyoyin da suke ganin su kadai za su iya share fagen inganta sha'anin almajiranci ga gwamnatocin da suka baiwa almajirai mazauni a jihohinsu.
Wasu jami’an tsaron Nijar biyu sun hadu da ajalinsu a wani dajin karamar hukumar Jibiya ta jihar Katsina lokacin da suke kokarin damke wasu ‘yan bindigar da suka sace shanu a kauyen Amore na karamar hukumar Dan Issa ta jihar Maradi.
Domin Kari