Kasar Sudan ta Kudu ta ayyana karshen annobar cutar kwalara a cikin kasar a hukumance, da ta barke a cikin kasar sama da watanni 18 da suka wuce, ta kama mutane sama da dubu 20 kana kuma ta kashe wasu 436.
Jiya Alhamis daruruwan masu zanga-zanga suka yi maci a babban birnin Kenya, suna neman shugaban kasa Uhuru Kenyatta ya ‘dauki mutane daga bangorori daban-daban a kasar a matsayin ministocinsa.
Shugaban na Amurka yace muddin 'yan majalisar dokoki ba zasu yarda da bukatarsa ta samar da karin kudaden kare bakin iyaka ba, to bai damu da a rufe ayyukan gwamnati ba.
Amma wasu daga cikin 'ya;yan jam'iyyar shugaban ta Republican da suka taka rawa wajen rubuta takardar sun musanta ikirarin Trump na cewa takardar dake sukar hujjojin binciken da hukumar FBI ta kaddamar ta wanke shi
Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Syria, Steffan de Mistura yace masu tattaunawa samun zaman lafiya a birnin Sochi na kasar Rasha, sun amince da kafa wani kwamitin da zai shirya daftarin sabon kundin tsarin mulkin kasar.
Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya a jiya Talata ya sabunta takunkumin makamai a kan jamhuriyar Afrika ta Tsakiya da shekarar guda, kuma yayi karin wani ma’aunin da zai kai ga karin sabbin takunkumai.
Dan majalisar wakilai Joe Kennedy na uku na jami’iyar Democrat mai wakiltan Massachusetts ya maida martani a kan jawabin shugaba Donald Trump yayi ga kasa.
Kungiyoyin sa kai a jihar Taraba arewa maso gabashin Najeriya sun yi kira ga sufeta Janar na yan sandan Najeriya da sauran shugabanin tsaro da su bincika rahotannin dake cewa an saki wasu da aka kama dake da hannu dumu dumu a tashin hankalin da ya auku a yankin Mambilla, makwannin baya.
A jawabinsa na farko akan halin da kasa ke ciki a jiya Talata, shugaban Amurka Donald Trump, ya yabawa sojojin Amurka.
Amurka ta karu da kawayenta na NATO a jiya Talata suka yi tir da amfani da makamai masu guba a kasar Syria, yayin da suka dora laifi a kan kasar Rasha mai bada kariya ga gwamnatin shugaban Syria Bashar al-Assad
Amurka ta fada a jiya Talata cewa, kafin karshen wannan shekara zata fidda tsarin tattaunawar zaman lafiyar yankin Gabas ta Tsakiya, sai dai mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence yace hakan zai ta’allaka ne a kan amincewar Falasdinu ta koma kan teburin tattaunawa da Isra’ila.
Wasu tagwayen bam baman cikin mota da suka tsahi sun kashe mutane akalla tara kana kuma suka jikata sama da wasu 30 a Benghazi na kasar Libya a jiya Talata.
A yau laraba ne dokar haramta kiwo da gwamnatin jihar Taraba ta kafa zata soma aiki, yayin da kungiyoyin makiyaya ke cewa ba zata sabu ba. Gwamnatin jihar tace ta kafa dokar ne domin samar da zama lafiya a tsakanin manoma da makiyaya.
Kungiyar Tarayyar Turai zata taimakawa jihar Borno ta sake gina jihar da sha fama da rikicin yan ta’addan Boko Haram. Kungiyar ta EU zata bada taimakon ne ta fannonin kiwon lafiya, ilimi, da ruwa mai tsafta da wutar lantarki da wasu abubuwar more rayuwa.
Jami’an leken asirin Amurka sun yabawa ‘yan majalisar dokokin kasar domin amincewa da shirin sa ido mai sarkakiya, da ‘yan fafatukar kare sirrin jama’a suke kushewa, da cewa, bai kare ‘yaancin talakawa ba.
Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa yace za a gudanar da zabe a kasar cikin watanni hudu zuwa biyar, wanda shine zai kasance na farko tun bayan hambare mulkin Robert Mugabe da ya dade bisa karagar mulki.
Tsofaffin jakadun Amurka a kasashen Afrika guda saba’in da takwas sun aikawa fadar shugaban Amurka ta White House da wasika, suna bayyana matukar damuwa dangane da kalaman batancin da aka ce shugaba Donald Trump ya yi inda ya kira kasashen Afrika kaskantattu.
Kungiyoyin fafatuka a Najeriya sun yi kira da a gaggauta tabbatar da daftarin shirin kasa a kan yan gudun hijira na cikin gida wato IDP don ya zama doka ta yadda za’a magance matsalolin da ‘yan gudun hijiran ke huskanta.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta cafke wasu mutane goma sha biyu, a ciki har da hakimin Gurmana, Alhaji Aliyu Umar bisa zarginsu da zama muggan masu garkuwa da mutane da kuma satar shanu a jihar Neja.
Domin Kari